05
Aug
Daga BASHIR ISAH Rundunar Sojan Nijeriya ta kafa kwamitin musamman don gudanar da bincike kan matuwar wani ɗan sanda da ake zargin soja ne ya kashe shi yayin rashin jituwar da aka samu tsakanin 'yan sanda da sojoji a Legas. Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Sashen Hulɗa da Jama'a na 81 Division, Manjo Olaniyi Osoba ne ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da aka raba wa manema labarai ranar Juma'a. Manjo Osoba ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta'aziyyar Rundunar Sojan Nijeriya ga iyalan marigayin, tare da ba da tabbacin rundunar za ta yi bincike domin gano haƙiƙanin gaskiyar abin…
