10
Jan
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa da naƙasassun da ke Nijeriya hanyoyin da za su riƙa bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin ƙasa da na mota da makarantu. Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Naƙasassu ta Ƙasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Hajiya Sadiya ta gode wa Shugaban Ƙasa saboda yadda ya amsa kiran naƙasassun…
