Labarai

’Yan bindiga sun hana jirgin sama tashi a Kaduna

’Yan bindiga sun hana jirgin sama tashi a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gungun ’yan bindiga sun hana wani jirgin saman AZMAN da ke shirin zuwa Legas tashi a ranar Asabar daga filin jirgin saman Kaduna. Wata majiya ta tabbatar da cewa ’yan bindigar sun harbe wani ma’aikacin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Saman Nijeriya (NAMA), Shehu Na’Allah a kusa da titin jirgin da ke filin jirgin. Majiyar ta bayyana cewa, jirgin na AZMAN bai iya tashi da misalin ƙarfe 12:30 na dare ba saboda kasancewar ’yan bindigar a titin filin jirgin. “Kamar yadda na ke magana da ku a yanzu, akwai sojoji da dama da ke sintiri…
Read More
’Yan jarida sun karrama gidan kangararru da gyaran hali a Jihar Bauchi

’Yan jarida sun karrama gidan kangararru da gyaran hali a Jihar Bauchi

Daga ABUBAKAR A. BOLARI Wata ƙungiyar 'yan jarida mai suna ROJOF (Rehabilitations and Orphanage Journalist Covering Forum Bauchi) da suke bayyana aikace-aikacen wani gidan gyaran hali da tarbiyyar kangararru a jaridu da kafafaen yaɗa labarai a jihar Bauchi mai suna 'Malam Kawu Youth Rehabilitation and Orphanage Centre' sun karrama gidan sakamakon gamsuwa da yadda yake gyara tarbiyyar matasan. Ƙungiyar ta karrama mamallakin gidan ne mai suna Dakta Abdullahi Muhammad Tahir da ake kira Malam Kawu, saboda yadda jama’a suka gamsu da yadda yake kula da kangararrun ‘ya’yan su da suka samu matsalar ƙwaƙwalwa sakamakon shaye-shaye da sauran su. A jawabin…
Read More
Gwamnatin Jigawa ta gudanar da rigakafin cutar dabbobi

Gwamnatin Jigawa ta gudanar da rigakafin cutar dabbobi

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa ta gabatar da rigakafin cutar dabbobi a Ƙaramar Hukumar Kaugama da ke jihar. A jawabin da ya gabatar a lokacin ƙaddamar da allurar rigakafin, shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Idris Mati Hadi ya jaddada ƙudurin sa na tallafa wa makiyaya domin inganta lafiyar dabbobin su. Ya kuma yi kira ga makiyaya da su kai dabbobin su cibiyoyin rigakafi mafi kusa da su domin cin gajiyar shirin. Shi ma a nasa jawabin, shugaban sashin aikin gona da albarkar ƙasa na yankin, Alhaji Ado Musa ya ce kimanin dabbobi dubu 35 da suka haɗar…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 50 a Giwa, Jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 50 a Giwa, Jihar Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun kai wasu manyan hare-hare kan ƙauyuka shida a Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka kashe gwamman mutane a yankunan. Gwamnatin Kaduna ta bakin Ma'aikatar Tsaro ta tabbatar da kai harin a ranakun Alhamis da Juma'a, amma ba ta bayyana adadin waɗanda aka kashe ba, tana mai cewa suna jiran cikakken rahoto kan lamarin. Wasu rahotanni da Manhaja ta tattara a ta bakin yadda mutanen yankin ke bayyanawa, sun ce an kashe mutum kusan 50 tare da yin garkuwa da fiye da mutum hamsin. Garuruwan da lamarin ya shafa sun…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: Masu neman shugabancin APC sun janye wa Abdullahi Adamu

Da ɗumi-ɗuminsa: Masu neman shugabancin APC sun janye wa Abdullahi Adamu

Ana gab da soma kaɗa ƙuri'a ne shida daga cikin 'yan takarar shugabancin jam'iyyar APC da suka shirya fafatawa da zaɓin Shugaba Muhammadu Buhari, suka miƙa wuya suka janye takararsu. Da wannan, ya tabbata cewa Sanata Abdullahi Adamu da ya kasance zaɓin Shugaba Buhari, shi ne zai zama shugaban jam'iyyar APC na ƙasa na gaba. Wasiƙar da ta nuna janyewar 'yan takarar Wata wasiƙa da ta sami sa hannun Sanata Geoge Akume, a madadin 'yan takarar ta nuna yadda baki ɗaya 'yan takarar suka yi wa zaɓin Buhari mubaya'a.
Read More
Yadda ’yan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara

Yadda ’yan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 25 da su ka haɗa da hakimi da kuma wasu sarakunan gargajiya a Ƙaramar Hukumar Bukkuyyum da ke a Jihar Zamfara a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya. 'Yan bindigar dai sun afka ƙauyen Ganar Kiyawa ne a ranar Lahadi kuma suka kashe mutanen, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC. Mutanen garin sun ce 'yan bindigar sun shiga garin na Ganar Kiyawa ne saman babura, kuma bayan mutane sun tsorata sun fara tserewa, 'yan bindiga suka dinga harbinsu, cikin waɗanda aka kashe har da hakimin garin Bala…
Read More
Kotu ta yanke wa karuwai 61 hukuncin wata shida a Jigawa

Kotu ta yanke wa karuwai 61 hukuncin wata shida a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Wata Kotun Majistare dake zamanta a Ƙaramar Hukumar Ringim, ta ɗaure wasu mata su 61 watanni shida ko tarar Naira 20,000 kowacce. Alƙalin kotun Mai Shari'a Sadisu Musa Jahun ne ya zartar da hukuncin a makon da ya gabata. An yanke musu hukuncin ne a laifin farko da ake tuhumarsu na aikata baɗala, inda kotu ta ce za su biyar tarar Naira dubu goma sha biyar ko wata uku a gidan gyaran hali. Sai laifi na biyu da ake tuhumarsu da shi shi ne laifin tada hankalin al'umma, wanda shi ma kotun ta zartar…
Read More
Hare-haren Kudancin Kaduna aiki ne na rashin hankali – Buhari

Hare-haren Kudancin Kaduna aiki ne na rashin hankali – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi allawadai da harin da 'yan ta'adda suka kai yankuna huɗu a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura ta Jihar Kaduna, inda suka kashe sojoji biyu da fararen hula 10, yana mai alaƙanta harin da "aiki na marasa hankali", wanda mutum wayayye mai hankali ba zai iya aikata shi ba. "Mummunan harin da 'yan ta'adda suka kai wa fararen hula da jami'an tsaron da ba su ji ba su gani ba da kuma ɓarnata gidaje da shaguna abin takaici ne da allahwadai. Ƙasa gabaɗaya tana miƙa ta'aziyyarta ga jama'an Kagoro, yankin…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: APC ta haramta wa Malami da takwarorinsa kaɗa ƙuri’a yayin babban taronta

Da ɗumi-ɗumi: APC ta haramta wa Malami da takwarorinsa kaɗa ƙuri’a yayin babban taronta

Daga BASHIR ISAH Kwamitin riƙo da shirya babban taro na jam'iyyar APC (CECPC) ya haramta wa masu riƙe da muƙaman siyasa yin zaɓe yayin babban taron jam'iyyar da zai gudana gobe Asabar. Cikin wani bayani da ya fitar a jiya Alhamis, kwmitin ya nuna cewa, "ɗaukacin masu riƙe da muƙaman siyasa waɗanda aka zaɓa a matsayin dalaget ga babban taron jam'iyya da zai gudana a ranar 26/3/2022 ba za su kaɗa ƙuri'a ba saboda dambarwar da ke tattare da sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe na 2022.” Amma duk da wannan matsayar da aka cimma, kwamitin ya ce waɗanda…
Read More
Shugaban Nijeriya ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama da Sin ta tallafa wajen ginawa a Legas

Shugaban Nijeriya ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama da Sin ta tallafa wajen ginawa a Legas

Daga CMG HAUSA Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama, a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed dake birnin Ikon jihar Lagos. Yayin ƙaddamarwar, shugaba Buhari ya ce an tsara sabon sashen ne, ta yadda zai riƙa karɓar fasinjoji miliyan 20 a duk shekara, yayin da kuma zai samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye har 3,000, da kuma wasu guraben da ba na kai tsaye ba. Shugaban ya ƙara da cewa, kammalar aikin ya buɗe wani sabon babi na sufurin jiragen sama, mai cike da tsaron lafiya da…
Read More