Kotu ta yanke wa karuwai 61 hukuncin wata shida a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Wata Kotun Majistare dake zamanta a Ƙaramar Hukumar Ringim, ta ɗaure wasu mata su 61 watanni shida ko tarar Naira 20,000 kowacce.

Alƙalin kotun Mai Shari’a Sadisu Musa Jahun ne ya zartar da hukuncin a makon da ya gabata.

An yanke musu hukuncin ne a laifin farko da ake tuhumarsu na aikata baɗala, inda kotu ta ce za su biyar tarar Naira dubu goma sha biyar ko wata uku a gidan gyaran hali. Sai laifi na biyu da ake tuhumarsu da shi shi ne laifin tada hankalin al’umma, wanda shi ma kotun ta zartar masu da hukuncin wata uku ko tarar Naira dubu goma.

Gaba ɗaya shi ne aka yanke masu hukuncin yin watanni shida a gidan gyaran hali ko tarar Naira 20,000 kowannen su.

Yayin da su kuma mazan su 17 da aka kama a gidajan karuwan aka yanke masu hukuncin wata biyu Ko tarar Naira dubu goma kowannen su.

A laifi na biyu da kotun take tuhumar mazan su ma kotun ta ɗaure su wata uku ko tarar Naira dubu goma sha biyar kowannen su, tare da sanya dukkansu su sanya hannu akan takaddar yarjejeniyar duk wadda aka sake kamawa aka gurfanar da shi a gaban kotun, kotun za ta rivanya ma sa hukunci za ta yi.