Shugabancin APC: Yadda Abdullahi Adamu ya yi fintinkau

*Abinda ya sa gwamnoni na miƙa wuya gare shi – Gwamnan Nasarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da tsare-tsare a taron Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi A. Sule, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnonin jam’iyyar suka amince wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan zaɓar tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaba na gaba na jam’iyya mai mulki.

A ranar gobe Asabar ne dai aka shirya gudanar da taron a Abuja.

Da ya ke zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen kwamitinsa gabanin zaɓen, Gwamna Sule, ya ce, waɗanda ke da ra’ayin ɗaukar Sanata Adamu a matsayin ɗaya daga cikin ’yan takara, a ƙarshe za su amince da zaɓin nasa, saboda irin mutuntawar da Buhari ke samu a tsakanin masu ruwa da tsaki.

Ya ce, “abin da jam’iyyarmu ke da shi da wasu ba su da shi, shi ne kasancewar muna da shugaban siyasa kuma uba wanda duk wanda ke cikin wannan jam’iyya da gaske ya ke mutuntawa, wato Shugaba Muhamadu Buhari.

“Mu na da yaƙinin cewa, ba zai yi wani abu ba don son kai kawai ko son zuciya ko wani abu da zai sava wa muradun jam’iyyar, yana da sha’awar tabbatar da haɗin kan jam’iyyar. Don haka ba ya yin wani abu, don amfanin kansa. Irin wannan shugaba da mu ke da shi, wanda hakan ya sa duk lokacin da ya yi magana kowa ke ji, domin kowa ya san ba don wani amfanin kansa ya ke yi ba, wannan ita ce buƙatarsa kuma ina gaya muku buƙatarsa za ta samu karɓuwa domin mun san duk abin da ya ke yi don amfanin jam’iyya ne,” inji shi.

Gwamnan Jihar Nasarawa ya kuma tabbatar wa jam’iyyar masu aminci cewa za a yi duk mai yiwuwa, don gamsar da sauran masu neman tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar da su sanar da janyewarsu a hukumance domin cika wasu tanade-tanade na dokar zaɓe.

Ya ce, “idan ku ka zo kan dokar zaɓe, mu jam’iyya ce mai bin doka da oda, za mu yi duk abin da ya dace a tsarin dokar zaɓe, ba za mu yi komai ba a matsayinmu na jam’iyyar siyasa da za a shiga karya doka ba, domin a matsayinmu na jam’iyya mai mulki ba za mu aiwatar da wani abu da zai cutar da dokarmu a ƙasar nan.

Ya kuma yi watsi da raɗe-raɗin cewa, Kwamitin Tsare-tsare na Riƙo na APC a ƙarƙashin jagorancin takwaransa na Jihar Yobe, Mai Mala Buni zai yi niyyar mayar da kuɗin takarar da ’yan takarar shugabancin jam’iyyar suka biya.

“Mayar da kudaden da aka biya ga masu neman takara; wannan roƙo ne da shugaban ƙasa ya yi don nuna jagoranci.”

Ya ce, “da zarar mun amince da yarjejeniya ya dace a mayar musu da abin da suka biya. Wata buƙata ce da a zahiri mai girma shugaban ƙasa ya gabatar ga shugabancin jam’iyyar kuma shugabancin na can. Don haka zan ce shugabannin jam’iyyar su ma sun amince.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *