Labarai

Zargin karkatar da kuɗaɗe: Kotu ta wanke Sanata Umar Tafida

Zargin karkatar da kuɗaɗe: Kotu ta wanke Sanata Umar Tafida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alƙalin babbar kotun Jihar Sakkwato, Mai shari’a Mohammed Mohammed a ranar Litinin ya kori shari’ar karkatar da kuɗaɗe da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'annati (EFCC) a madadin gwamnatin tarayya ke yi wa Sanata Umar Tafida tare da sallamar Sanata Tafida babu laifi. A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Mohammed ya caccaki EFCC a matsayin mai shiga tsakani da ta ƙi yin aikinta kafin ta gurfanar da mutane a kotu. A cewar mai shari’a Mohammed, EFCC ta gaza bin ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa wajen gabatar da tuhumar da ake wa…
Read More
An samu rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa game da hukuncin kotu kan Dokar Zaɓe

An samu rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa game da hukuncin kotu kan Dokar Zaɓe

Daga WAKILINMU An samu rarrabuwar kawuna yayin zaman sanatoci a wannan Talatar dangane da kiran da aka yi wa Majalisar Dattawa na tafka muhawara kan hukuncin da Babbar Kotu ta yanke game da haramta Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe. Rikicin ya soma ne sa'ilin da Sanata George Sekibo daga jihar Rivers, ya dogara da doka ta 10 da ta 11 na dokokin majalisa wajen nusar da takwarorinsa irin ayyukan da suka rataya a kan sassa ukun da gwamnati ke da su, wato ƙananan hukumomi, jihohi da kuma gwamnati tarayya. Ya ce hukuncin da kotun ta yanke na sauke matakin…
Read More
‘Yan sanda sun cafke matar da ake zargi da babbake ‘yarta a Ogun

‘Yan sanda sun cafke matar da ake zargi da babbake ‘yarta a Ogun

Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wata mata mai suna Aisha Tijani bisa zargin babbake 'yarta. Wacce ake zargin ta faɗa a komar 'yan sanda ne biyo bayan ƙarar da wani mai suna Moroof Ayinde ya shigar a ofishin 'yan sanda na yankin Mowe a jihar. Ayinde ya faɗa wa 'yan sanda cewa a gida ɗaya suke zaune da matar da ake zargi da babbake 'yarta 'yar shekara 10 da haihuwa. A cewarsa, matar ta fusata ne bayan da yarinyar ta ɗauki wayar da ta ƙwace daga hannun ɗaya daga cikin 'ya'yanta ta ɓoye sannan ta…
Read More
Buhari ya amince da sake fasalin hukumar NBC

Buhari ya amince da sake fasalin hukumar NBC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin kwamitin gudanarwa ta Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC). Hakan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin tsohon kwamitin kamar yadda rahotanni suka bayyana. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Bashir Bolarinwa ne sabon shugaban kwamitin. Ya ce wani wakilin rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), wani wakilin ma’aikatar labarai da al’adu da kuma darakta janar na hukumar su ma mambobi ne a kwamitin. Sauran mambobin su ne Wada Ibrahim, Iheanyichukwu…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta cire tallafin Naira biliyan 600 na wutar lantarki

Gwamnatin Nijeriya ta cire tallafin Naira biliyan 600 na wutar lantarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Samar da.Wutar Lantarki a Nijeriya (NERC), ta ce gwamnatin tarayya ta janye tallafin wuta. Raranar Larabar da ta gabata an jiyo hukumar NERC ta na cewa tallafin shan wutar da ya ci wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 600 ya zo ƙarshe a halin yanzu. NERC ta bada sanarwar ƙara farashin shan wutar lantarki a Fabrairun wannan shekara ta 2022. An ɗauki wannan mataki ba tare da wani vata lokaci ba. Hakan na zuwa ne a lokacin da kamfanonin da ke samar da wuta su ka soki aikin NBET, suka ce kamfanin ya gagara…
Read More
2023: Abinda Obasanjo ya shaida min game da shugabancin Igbo – Ohuabunwa

2023: Abinda Obasanjo ya shaida min game da shugabancin Igbo – Ohuabunwa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi A ƙoƙari da ya ke yi na cimma burinsa na kasancewa Shugaban Tarayyar Nijeriya, wani ɗan takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Mazi Sam Ohuabunwa, makon da ya gabata ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo a garinsu na Abeokuta dake cikin jihar Ogun. Mai neman takarar shugabancin ƙasar, ya kuma ziyarci dattawa da shugabanni na jam’iyyar PDP dake jihar ta Ogun, a cikin ziyarce-ziyarcen kamun ƙafa da yake yi. Da yake yi wa manema labarai jawabi, jim kaɗan bayan ganawar su ta sirri da tsohon shugaban ƙasan, Ohuabunwa ya ce, ya je Abeokuta ne domin…
Read More
Zan yi murabus a mutunce idan lokaci ya yi – Malami

Zan yi murabus a mutunce idan lokaci ya yi – Malami

Daga SANI AHMAS GIWA a Abuja Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga kujerarsa ba, inda ya bayyana cewa zai kammala wa’adin mulkinsa a mutunce a watan Mayun 2023. Malami ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, 17 ga watan Maris, a Abuja yayin da yake jawabi a wani taro da ƙungiyar masu aiko da rahotanni na shari’a ta ƙasa suka shirya. Ministan ya yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai na cewa ya yi murabus daga kujerarsa, yayin da ya buƙaci manema labarai da su kasance masu gaskiya a rahotanninsu.…
Read More
Sojoji sun ga bayan jagoran ISWAP, Shuwaram a wani samame

Sojoji sun ga bayan jagoran ISWAP, Shuwaram a wani samame

Daga BASHIR ISAH Jagoran mayaƙan ISWAP, Sani Shuwaram tare da wasu dakarunsa sun cimma ajalinsu a wani luguden wuta da sojojin saman Nijeriya suka yi musu a yankin Marte. Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna jirgin yaƙin sojojin Nijeriya Super Tucano da dauransu ne suka yi wa sansanin Shuwaram ruwan bamabamai inda aka halaka mayaƙan da damansu. An ce Shuwaram ya cimma ajalinsa ne sakamakon ranukan da ya ji daga harbin bindiga a lokacin da sojoji suka farmaki sansanin ISWAP da ke Sabon Tumbuns a yankin Tafkin Chadi. Wani babban jami'in sojoji ya tabbatar wa jaridar PRNigeria nasarar…
Read More
Gwamnatin Jigawa ta kashe Naira miliyan 40,000 wajen biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu

Gwamnatin Jigawa ta kashe Naira miliyan 40,000 wajen biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta biya haƙƙoƙin ma’aikatan jihar kusan miliyan dubu 40 daga watan Mayu na 2015 zuwa Maris na shekarar 2022. Sakataren zartarwar hukumar asusun adashen gata na jihar, Alhaji Kamilu Aliyu Musa, ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewar, adadin kuɗin ya tasamma fiye da Naira miliyan dubu talatin da tara da miliyan ɗari tara da goma sha takwas a matsayin haƙƙoƙin ma’aikatan. Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya ce haƙƙoƙin ma’aikatan da asusun ya biya a waɗannan shekaru sun haɗar da giratuti ga…
Read More
Gobara ta tashi sau 15 a jere a unguwar Danbare a Kano

Gobara ta tashi sau 15 a jere a unguwar Danbare a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata mata mai suna Hajiya Hauwa Mai-kitso da ke zaune a unguwar Danbare B da ke Ƙaramar Hukumar Kumɓotso a Jihar Kano ta koka akan yadda gobara ta addabe ta. Gobarar wacce ya zuwa yanzu ba a san daga ina matsalar ta ke ba, amma al'umma sun fara hasashen cewa ko aljanin nan mai suna Batoyi ne ke haɗa mata gobarar, duba da cewa wutar ce ka tashi ba tare da wani musabbabi ba. A zantawarsa da manema labarai Hajiya Hauwa ta ce sau goma sha biyar kenan wutar na tashi, inda ta ce ko…
Read More