Labarai

Jami’an Hisbah sun ƙwace katan-katan na giya a Kebbi

Jami’an Hisbah sun ƙwace katan-katan na giya a Kebbi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Jami’an Hukumar Hisbah a jihar Kebbi ranar Asabar da ta gabata ne suka ƙwace katan-katan na nau’in giya daban-daban a Birnin Kebbi, helkwatar jihar. Ma’aikatan na hisbah waɗanda suka yi amfani da wasu bayanan sirri suka dira wa wani saƙo kusa da tsohuwar kasuwa inda suka riski wata mota an cika ta tab da barasa kuma tana ƙoƙarin zuwa kasuwanci lokacin da suka ritsa ta. Wannan dabara ta yin kasuwancin giya, kamar yadda kwamandan hisbah na jihar ya bayyana, ya yi bambaraƙwai da dokokin jihar Kebbi waɗanda suka hana fatauci da shan barasa a ɗaukacin…
Read More
NAPTIP ta ceto ƙananan yara 30 daga hannun miyagu cikin shekara guda

NAPTIP ta ceto ƙananan yara 30 daga hannun miyagu cikin shekara guda

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa (NAPTIP), ta umurci duka shiyyoyin ta dake duka jihohin ƙasar nan da su fara gudanar da sintiri na musamman cikin gaggawa a yankunan su don tabbatar an cafke duka waɗanda ke safarar yara ƙanana, ciki har da waɗanda ke da hannu cikin harkokin saya da sayar da mutane don su fuskanci hukuncin doka.  Darakta Janar ta hukumar, Dr. Fatima Warizi-Ari ce ta ba da umurnin a cikin wata takardar jawabin harkokin hukumar cikin shekara ɗaya, wanda daraktar ta sanya hannu sa’anan mai magana da yawun hukumar Misis…
Read More
Matar Marigayi Ojukwu da ta gwamnan Anambara mai barin gado sun tsinke juna da mari a taro

Matar Marigayi Ojukwu da ta gwamnan Anambara mai barin gado sun tsinke juna da mari a taro

Daga AISHA ASAS a Abuja Kallo ne ya koma sama a wajen rantsar da Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuka Soludo, a jiya Alhamis, bayan da matar gwamna mai barin gado, Obelechukwu Willie Obiano, ta tsinka wa Bianca Ojukwu mari a bainar jama'a, inda nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan da gwamnan mai jiran gado, Farfesa Soludo, ya ɗauki rantsuwar kama aiki. Kamfanun NAN ya ruwaito cewa, manyan baƙi su na zazzaune lokacin da mai-ɗakin Obiano ta iso. Tana shigowa, ta na taku ɗaiɗai sai…
Read More
Dalilinmu na naɗa hadimin Gwamnan CBN sarautar Ɗan Amanan Bauchi – Sarkin Bauchi

Dalilinmu na naɗa hadimin Gwamnan CBN sarautar Ɗan Amanan Bauchi – Sarkin Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, ya bayyana amana a matsayin wani babban nauyi ne wanda ya jiɓanci kowane bani adam, amma kuma kaɗan ne daga cikin mutane a cikin al’umma suke iya riƙewa. Sarkin Bauchi ya bayyana cewar, fadar sa ta ɗauki tsawon lokaci tana jimamin wanda ya kamata ya ɗauki ko riƙe wannan matsayi na sarautar Ɗan Amanan Bauchi daga cikin masarautar, sai yanzu da Allah ya bayyana Dokta Ahmad Shehu a matsayin mutumin da ya dace ya riqe amanar, ba masauratar Bauchi kaɗai ba, har ma da jiha, Nijeriya da…
Read More
Kotu ta Janye karya belin Muaz Magaji a Kano

Kotu ta Janye karya belin Muaz Magaji a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kotun Majistiri mai 58 ta dakatar da karya belin da ta baiwa Engr. Mu'az Magaji Ɗan-Sarauniya a ranar Litinin da ta gabata, Tun da fari dai, kotun ta karya belin da ta baiwa Ɗan-Sarauniya ɗin ne sakamakon ƙin halartar kotu da ya yi, daga bisani kuma sai ta janye karya belin wanda daga bisani ya halarta. A ranar juma'a da ta gabata da safe Magaji ya je kotun, ya yi ta jira har zuwa da rana, amma da ga bisani sai alƙalin ya shaida wa jami'in kotun cewa ba zai samu damar zama ba. Sai…
Read More
Ɗan jarida, Agba Jalingo, ya bayyana taskun da ya shiga a hannun Abba Kyari

Ɗan jarida, Agba Jalingo, ya bayyana taskun da ya shiga a hannun Abba Kyari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wani mawallafin jarida mai suna ‘CrossRiverwatch’ kuma ɗan gaba-gaba dai, Agba Jalingo a ranar Litinin da ta gabata ne ya kwance bakin jaka dangane da azabar da ya ɗanɗana a hannun kamammen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da yaransa, lokacin da aka kama shi, haɗi da ɗauko shi tun daga Legas zuwa Kalaba a cikin mota, cikin wani mawuyacin hali. Ya yi tuni da cewar, an kama shi ne dangane zargin cin amanar ƙasa bisa umarnin gwamnatin jihar Kuros Ribas, kuma an damƙe shi ne a ranar 22 ga watan Agusta na shekarar 2019,…
Read More
Ku daina ci wa junanku dunduniya, Buhari ga gwamnonin APC

Ku daina ci wa junanku dunduniya, Buhari ga gwamnonin APC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari has ya gargaɗi gwamnonin jam'iyyarsu ta APC) kan su guji ci wa junansu dunduniya dangane da sha'anin babban taron jam'iyyar wanda zai gudana ran 26 ga Maris. Gargaɗin Buhari na da nasa da yadda wasu gwamnoni suna karaɗe kafafen yaɗa labarai da ambaton suna da furta kalmomi marasa dattako kan ɗaya daga cikinsu, wato Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe. Wasu takwarorin Gwamna Buni kuma shugaban kwamitin riƙo da shirya babban taron jam'iyya (CECPC), sun nuna ba Buni ne shugaban riƙo kuma ba, tare da ambaton Gwamnan Neja, Sani Bello a matsayin…
Read More
Duk da dokar taɓaci kan ilimi a Sakkwato, firamare ta Ruggar Giwa na cikin wani hali

Duk da dokar taɓaci kan ilimi a Sakkwato, firamare ta Ruggar Giwa na cikin wani hali

Daga AMINU ALHUSSAIN AMANAWA a Sakkwato Makarantar firamaren Ruggar Giwa dai na a ƙauyen Tuntube ne dake yamma da garin Shuni na ƙaramar hukumar mulkin Dange-shuni dake jihar Sakkwato, tafiyar aƙalla mintuna 15 zuwa 20 daga ƙauyen zuwa ƙwaryar birnin Sakkwato. Makarantar wacce aka kafa sama da shekaru 40 da suka gabata, na cigaba da kasancewa cikin halin ka’ka’ni kayi, na lalacewar ajijuwa, da ofishin shugaban makaranta, da ma na malamai, uwa uba rashin kayan rubutu da na karatu da makarantar firamaren ke fama da shi. A cewar ɗaya daga mazauni ƙauyen Malam Muhammad Naira Tuntube, yanayin da makarantar ke…
Read More
ASUU ta ƙara mako takwas a kan yajin aikin da take yi

ASUU ta ƙara mako takwas a kan yajin aikin da take yi

Daga SANI AHMAD GIWA Yayin da a yau Litinin wa'adin yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) take yi, ƙungiyar ta kuma sanar da tsawaita yajin aikin da makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan buƙatunsu. ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka ƙulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a a ƙasar. Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau, jami’i ne a ƙungiyar ta ASUU, ya ce sun ɗauki matakin ƙara wa’adin…
Read More
Sanata ya tallafa wa makarantar marayu a Kebbi

Sanata ya tallafa wa makarantar marayu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirinsa na tallafa wa marasa galihu Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ya tallafa wa makarantar marayu da ke ƙarƙashin kulawar 'Mar'atussaliha' ƙungiyar nan ta mata mai rajin kare mutuncin zawarawa da marayu da ke garin Argungu a jihar Kebbi da kayan aiki. Da ya ke jawabi lokacin miƙa kayan shugaban kwamitin gudanarwa na siyasar sanatan, Alhaji Aliyu Gandu Augie ya bayyana cewa wannan aikin ba sabon ba ne ga duk ɗan wannan yankin saboda kamar yadda kowa ya…
Read More