Ku daina ci wa junanku dunduniya, Buhari ga gwamnonin APC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari has ya gargaɗi gwamnonin jam’iyyarsu ta APC) kan su guji ci wa junansu dunduniya dangane da sha’anin babban taron jam’iyyar wanda zai gudana ran 26 ga Maris.

Gargaɗin Buhari na da nasa da yadda wasu gwamnoni suna karaɗe kafafen yaɗa labarai da ambaton suna da furta kalmomi marasa dattako kan ɗaya daga cikinsu, wato Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Wasu takwarorin Gwamna Buni kuma shugaban kwamitin riƙo da shirya babban taron jam’iyya (CECPC), sun nuna ba Buni ne shugaban riƙo kuma ba, tare da ambaton Gwamnan Neja, Sani Bello a matsayin sabon shugaban riƙo na kwamitin CECPC.

An ji Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya caccaki Buni a cikin wani shirin tashar Channel Television a Larabar makon jiya kan wai Bunin na ƙoƙarin dagula lissafin babban taron jam’iyya.

Cikin wata sanarwar ta hannun mai magana da yawunsa Garba Shehu a ranar Asabar da ta gabta, Buhari ya yi gargaɗin irin sakamakon da ka biyo bayan yadda shugabannin ke amfani da kafafen yaɗa labarai suna ci wa junansu dunduniya.

Buhari ya buga wa gwamnonin misali da gwamnoni PDP, jam’iyyar da ta yi mulki na tsawon shekara 16 amma daga bisani suka tsinci kansu cikin wani hali na rashin haɗin kai da sauransu. Ya ce ya kamata gwamnonin APC su ɗauki darasi daga hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *