Sojoji sun ga bayan jagoran ISWAP, Shuwaram a wani samame

Daga BASHIR ISAH

Jagoran mayaƙan ISWAP, Sani Shuwaram tare da wasu dakarunsa sun cimma ajalinsu a wani luguden wuta da sojojin saman Nijeriya suka yi musu a yankin Marte.

Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna jirgin yaƙin sojojin Nijeriya Super Tucano da dauransu ne suka yi wa sansanin Shuwaram ruwan bamabamai inda aka halaka mayaƙan da damansu.

An ce Shuwaram ya cimma ajalinsa ne sakamakon ranukan da ya ji daga harbin bindiga a lokacin da sojoji suka farmaki sansanin ISWAP da ke Sabon Tumbuns a yankin Tafkin Chadi.

Wani babban jami’in sojoji ya tabbatar wa jaridar PRNigeria nasarar da sojojin suka samu a kan Shuwaram da sauransu a yankin Arewa-maso-gabas.

A cewar majiyar, “Shuwaram na ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan da sojoji suka ji wa rauni yayin samamen da suka kai Sabon Tumbuns kusa da Kirta Wulgo a Fabrairun 2022. Akwai yiwuwar har-haren da suka biyo bayan nan sun yi tasiri wajen kashe Shuwaram da sauran mayaƙan ISWAP a inda ake kula da lafiyarsu, ciki har da Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi.”

Kawo yanzu dai an zaɓi wani Malam Bako Gorgore a matsayin magajin Shuwaram wanda zai ci gaba da jan ragamar harkokin ISWAP.

Da aka nemi jin ta bakinsaa, mai magana da yawun sojojn sama na ƙasa, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ƙi cewa komai kan mutuwar Shuwaram, amma ya ce mayaƙansu sun yi gagarumar nasara a kan ‘yan ta’addan a Tumbuns kusa da Kirta Wulgo a cikin ƙaramar hukumar Marte da ke yankin Tafkin Chadi.