26
Nov
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sashen Tactical Operatives tare da haɗin gwiwar FIB/STS ƙarƙashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, sun kama wata mata mai suna Fatima Lawali ‘yar shekara 30 da ta amsa laifin yin safarar harsasai ga ‘yan bindiga a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba N. Elkana ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a. A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a unguwar Gada Biyu da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bunguɗu a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ya ce, “A ranar 25 ga Oktoba,…
