Boko Haram sun saki sabon bidiyon wasu mutum 4 da ke hannunsu

Daga WAKILINMU

Mayaƙan Boko Haram sun saki wani bidiyo mai ɗauke da wasu mutum huɗu da suka kama daga sassan yankin Arewa-maso-gabas a Nijeriya.

Waɗanda aka gani a cikin bidiyon mai tsayin minti 1 da sakan 40 sun haɗa da Imranu Mohammed Askira, mai gonar kaji, da wani ma’aikaci mai aiki tare da NDA waɗanda aka kama su tsakanin Buratai da Buni Yadi a ranar 21/11/2021.

Sai kuma Zakariya Ajikime ma’aikacin UNICEF, wanda ya faɗa a hannun Boko Haram tsakanin Sabon gari da Wajoroko a ranar 3/10/2021.

Shi kuwa Mohammed Askira ma’aikacin Bankin Premier Commercial a Maiduguri, ya faɗa a komar Boko Haram ne ran 6/11/2021.

Yayin da Yusuf Nasiru wanda ma’aikaci ne a Hukumar Kiyaye Haɗurra, ya faɗa a hannun mayaƙan a ranar 2/11/2021.

Duka waɗanda aka yi garkuwar da su kowannensu ya faɗa da bakinsa yadda aka yi ‘yan bindigar suka kama shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *