Labarai

Wani mutum ya kashe almajiri, ya cire ƙwaƙwalwarsa a Bauchi

Wani mutum ya kashe almajiri, ya cire ƙwaƙwalwarsa a Bauchi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani mutum ya yi amfani da dutse wurin fashe kan wani almajiri mai shekaru 11 tare da cire ƙwaƙwalwarsa a yankin Ƙofar Wambai da ke cikin birnin Bauchi. Mazauna yankin sun ce, wani baƙo ne da ba a san ko wanene ba ya kira wasu ɗaliaban almajirai biyu tare da jan su zuwa wani keɓantaccen wuri inda ya aikata aika-aikar. Ɗaya daga cikin almajiran wanda ya sha da ƙyar, ya sanar da mazauna yankin abinda ya faru kuma sun hanzarta zuwa wurin amma sai suka tarar da gawar almajirin inda daga bisani suka sanar da 'yan…
Read More
WAEC ta saki kashi 80 na sakamakon jarrabawar 2021

WAEC ta saki kashi 80 na sakamakon jarrabawar 2021

Daga BASHIR ISAH Hukumar shirya jarrabawa ta WAEC ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na 2021. Shugaban WAEC a Nijeriya, Patrick Areghan, shi ne ya bayyana sakin sakamakon a ranar Litinin. Areghan ya ce adadin ɗalibai 1,573,849 ne suka yi rajistar WASSCE a tsakanin makarantu 19,425 da hukumar ta amince da musu, yayin da ɗalibai 1,560,261 ne suka rubuta jarrabawar. A cewarsa, ɗalibai 1,274,784 ne suka samu makin 'Credit' zuwa sama da haka a tsakanin darussa biyar haɗa da darasin Ingilishi da na lissafi, sannan ɗalibai 1,560,261 sun samu ƙasa da haka. Ya ƙara da cewa, an riƙe sakamakon…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara na APC a 2019

Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara na APC a 2019

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun harbe dan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2019 har lahira a jihar Zamfara akan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Rahoton ya ce, lamarin ya faru ne a ƙauyen Rijana da yammacin jiya Lahadi. Tuni jami'an tsaro suka kai gawar marigayi Sagir Hamidu Gusau asibitin garin Kaduna inda ake sa ran a miƙa gawar ga iyalan mamaci a yau Litinin da safe domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Read More
Yadda ɗan uwana ya cika a gabana – Aliko Ɗangote

Yadda ɗan uwana ya cika a gabana – Aliko Ɗangote

Daga BASHIR ISAH Hamshaƙin ɗan kasuwar nanAlhaji Aliko Ɗangote, ya bayyana yadda ƙaninsa, Marigayi Sani ya cika a gabansa a asibitin Amurka. Ɗangote ya ce likitoci sun sanar da shi cewa ɗan'uwasa zai cika cikin sa'a guda, kuma abin da ya faru kenan da lokacin ya cika, "Inda na ga na'aurar da aka maƙala masa take taimaka masa ta rinƙa ja da baya da aiki har ta kai ga ta tsaya." Ɗangote ya bayar da wannan labari mai cike da tausayi ne a lokacin da jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Alhaji Bola Tinubu, ya kai masa ziyarar ta'aziyya a Kano…
Read More
Matashiyar da aka taɓa zargi da safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudiyya ta kammala makarantar NDLEA

Matashiyar da aka taɓa zargi da safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudiyya ta kammala makarantar NDLEA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Zainab Habibu Kila, wacce hukumomin Saudiyya suka zarga da safarar ƙwayoyi a shekarar 2018, a ranar Juma’ar da ta gabata ta kammala karatunta a makarantar horar da dabarun kama miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) da ke Jos. Mahaifinta, Habibu Kila ya raba hotunan bikin yaye ɗaliban yayin da yake godiya ga Allah. An tuhumi Zainab Kila bisa kuskure da laifin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar Saudiyya a shekarar 2018, kuma an tsare ta na kwanaki kafin gwamnatin Nijeriya ta shiga tsakani aka sake ta. Wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce ta tsara matar ’yar Jigawa…
Read More
Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Keffi ta yi bikin yaye ɗalibai

Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Keffi ta yi bikin yaye ɗalibai

Daga BASHIR ISAH Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta yi bikin yaye ɗalibai da suka kammala difloma a fannin kimiyyar abinci (Nutrition and Dietetics). Bikin yayewar ya gudana ne a ranar Larabar da ta gabata a babban zauren taron kwalejin a sabon gininta da ke yankin Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Keffi, inda aka yaye tare da rantsar da ɗalibai su sama da sittin a matsayin cikakkun mabobin Ƙungiyar Masana Kimiyyar Abinci ta Nijeriya (IDN). Tun farko a jawabinsa na maraba, shugaban kwalejin, Suleiman A. Muhammad ya ce wannan shi ne karon farko da makarantar…
Read More
Marigayi Yusuf Maitama Sule bai saci Kwabon al’umma ba – Jega

Marigayi Yusuf Maitama Sule bai saci Kwabon al’umma ba – Jega

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfasa Attahiru Jega, ya shaida cewa, Marigayi Ɗanmasanin Kano, AlhajiYusuf Maitama Sule bai yi almubazaranci ko satar kuɗaɗen jama’a ba a lokacin rayuwar sa da ya riƙe muƙaman gwamnati daba-daban, tun yana ƙuruciyar sa. Fitaccen malamin jami’a Jega, ya yi wannan furuci ne yayin gudanar da wata lakca kan shugabanci domin girmama Marigayi Ɗanmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule wadda gamayyar ɗaliban arewacin ƙasar nan ta shirya, wanda aka gudanar a cibiyar Umaru Musa Yar’adua da ke Jami’ar Katsina a ranar Litinin da ta…
Read More
Kunama ta buwayi mutane bayan tafka ruwan sama a Masar

Kunama ta buwayi mutane bayan tafka ruwan sama a Masar

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliya ya sauka a Aswan na ƙasar Masar, inda ya koro wasu irin nau’ukan kunamai masu haɗari zuwa neman mafaka a gidajen mutane. Mutane 3 ne AlJazeera ta ruwaito suka mutu inda sama da 400 ke kwance a asibiti a faɗin jihar domin karɓar maganin dafin kunama, a cewar kafafen yaɗa labarai na gwamnati. Sai dai kuma muƙaddashin ministan lafiya na ƙasar, Khalid Abdel-Ghafar, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, ba a samu rahoton mace-mace ko ɗaya ba. Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta tabbatar wa da jama’a cewa, tana…
Read More
An gano wanda ya sace Naira Miliyan 88.1 bayan shekaru 52

An gano wanda ya sace Naira Miliyan 88.1 bayan shekaru 52

Theodore John Conrad, wani mutum mai shekaru 20 a watan Yulin 1969, a lokacin ya fara aiki a wani banki da ke Amurka. Bayan fara aikin ne ya sace Dala 215,000, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 88,182,250 a kuɗin Nijeriya, daga nan babu wanda ya sake ganin sa. CNN ta ruwaito yadda darajar kuɗin da ya sata a yanzu ta kai $1.7m (N697,255,000) wanda shi ne mafi girman sata da aka taɓa yi wa banki a tarihin duniya. Ya koma wani garin fiye da shekaru 50 da suka shuɗe daga baya ’yan sanda su ka bayyana cewa ranar…
Read More
Ban ɗau fiye da mintuna uku ba kacal, inji mai fyaɗe

Ban ɗau fiye da mintuna uku ba kacal, inji mai fyaɗe

Wani mai fyaɗe, Sangokunle Akintola, wanda ya raka abokinsa Ismaila Raimi, domin koya wa wata budurwa darasin da ba za ta taɓa mantawa ba, ya shaida wa ’yan sandan jihar Osun cewa, bai wuce mintuna uku ba a lokacin da ya ke yi wa budurwar fyaɗe. Ismaila ya kasance yana abota da yarinyar tsawon wata shida, yana ba ta kuɗi masu yawa kuma yana fatan ya aure ta a gaba. Sai dai da yarinyar ta ce masa bai dace da damfara ba ‘Yahoo’, sai ya sha tabar wiwi, ya ɗauki sanda ya yi amfani da shi a matsayin bindiga ya…
Read More