Labarai

Gwamnan Adamawa ya fifita cigaban ilimi a jiharsa – Sakataren Ƙungiyar Malamai

Gwamnan Adamawa ya fifita cigaban ilimi a jiharsa – Sakataren Ƙungiyar Malamai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD Duk da matsaloli da barazanar tsaron da ake fuskanta a arewacin Nijeriya, ba a taɓa daina zuwa makarantu a Jihar Adamawa ba, saboda yadda gwamnan jihar, Ahmad Fintiri, ya fifita harkokin ilimi a jihar. Sakataren ƙungiyar malamai ta ƙasa reshen jihar ta Adamawa, Kwamared  Wakili Kyari ne ya bayyana haka a Kano a yayin taron shekara-shekara na ƙasa da ƙungiyar shugabannin makarantun firamare suka gudanar. Ya ce Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Fintiri yana bada kulawa sosai ga ci gaban ilimi fiye da gwamnoni da suka gabata, duk da matsalolin da ba za a rasa ba. Domin kafin zuwansa malamai…
Read More
An nemi manoma su daina sarrafa amfanin da ke sanya cuta

An nemi manoma su daina sarrafa amfanin da ke sanya cuta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An buƙaci manoma da su kiyaye da yadda za a sarrafa kayan amfanin gona bayan sun yi girbi domin kawo ƙarshen yadda a wani lokaci abincin ya kan zama sanadiyyar jawo cututtaka ga al’umma, matuƙar ba su yi amfani da shawarwarin masana harkar noma ba. Farfesa Sani Miko, Shugaban Hukumar Sasakawa ta Nijeriya ne ya yi wannan kiran a yayin da ma’aikatar sa ta Sasakawa ta shirya wata bita mai taken 'hada-hada kan kayan noma bayan girbi da kuma yadda za a ajiye shi.' Ma’aikatar ta shirya bitar ne ga manoman jihar Kano da…
Read More
Gidan rediyon Vision ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna

Gidan rediyon Vision ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Kamfanin yaɗa labarai na ‘Vision Media Service’, masu gidajen rediyon Vision FM ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna ta hanyar yaɗa jita-jitar ƙarya a kafafen sadarwa na zamani. A cikin wata sanarwa da babban jami’in gudanarwar kamfanin, Malam Shuaibu Mungadi, ya sanya wa hannun kuma ya raba wa manema labarai, ya ce, “abubuwan da ke faruwa a kafafen sadarwa na zamani dangane da kamfaninmu mai daraja, ya sa hukumar kamfanin ta fitar da wannan sanarwa da nufin gyara kura-kuren da wasu tsirarun mutane da wasu abokan aikin kamfanin suka yi.” Sanarwar…
Read More
Yadda aka kashe mutum 64 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Yadda aka kashe mutum 64 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Aƙalla mutum 64 ne aka kashe a cikin kwanaki biyu a jihar Sokoto yayin da ’yan bindiga suka kai farmaki. Adadin waɗanda suka mutu a hare-haren na ranar Lahadi da Litinin a ƙaramar hukumar Goronyo da ke jihar ya ƙaru zuwa 43 daga 15, yayin da wasu 14 suka mutu a ranar Talata a hare-haren da aka kai a ƙauyukan ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar. Harin na baya-bayan nan wanda aka kashe mutane 14 ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tura ƙarin kayan aikin soji…
Read More
Gwamnatin Kano ta biya Ja’afar Ja’afar diyyar ɓata sunansa

Gwamnatin Kano ta biya Ja’afar Ja’afar diyyar ɓata sunansa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta baiwa shahararren Dan jaridar nan Ja'afar Ja'afar Naira 800,000 saboda ɓata masa suna da ta yi, Jiya Juma'a ne dai Ja'afar Ja'afar ya sanarwa Freedom Radio Kano cewa, an biya shi kudin, kamar yadda kotu ta bada umarni da a biya shi Naira dubu 800, Tun a watan Yulin wannan shekarar ne dai babbar kotun Kano mai lambar 9 da ke zaman ta a Bampai ƙarƙashin mai Shari'a Baba na Malam ta umarci gwamnatin Kano ta biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa ƙudin, saboda ɓata masu…
Read More
Yadda kiran waya ya haifar da gobarar gas a Legas

Yadda kiran waya ya haifar da gobarar gas a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Talata a wani mummunar fashewar gas a kan titin Ojekunle, kusa da titin Ladipo, a unguwar Mushin da ke jihar Legas. Kamar yadda rahotanni suka ruwaito, bam ɗin ya lalata motoci aƙalla 15, tare da lalata gidaje da dama a yankin. Wurin da gobarar ta afku ya haɗa da makanikai, masu facin taya, dillalan iskar gas da sauran ’yan kasuwa. Shaidun gani da ido da suka zanta da kamfanin dillancin labarai, sun ce, lamarin ya faru ne a kusa da wata Mama Emma, mai soyan ƙosai da…
Read More
Gwamnatin Neja ta bayyana wuraren da Boko Haram ke iko da su a jihar

Gwamnatin Neja ta bayyana wuraren da Boko Haram ke iko da su a jihar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Matane ya bayyana cewa, ’yan ta'addar Boko Haram sun ƙwace garuruwa biyar a qananan hukumomin Rafi da Shiroto a jihar Neja. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Minna, babban birnin jihar a ranar Litinin. Ya yi bayanin cewa, mayaƙan na Boko Haram suna da cikakken iko a Hanawanka, Madaka, a ƙaramar hukumar Rafi da Kurebe, Gussau, Farina Kuka a ƙaramar hukumar Shiroro, wanda hakan ya tilasta wa mazauna karkara yin hijira zuwa wasu wurare. Ya ce, ’yan ta’addan na tafiya cikin…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta ba wa gwamnati wa’adin sati uku

Da ɗumi-ɗumi: ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta ba wa gwamnati wa’adin sati uku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin makonni 3 don cika ma ta sharuɗɗan da ta gindaya wa gwamnatin. Ta bayyana wannan ƙudirin nata ne inda ta ce wajibi ne gwamnatin ta cika ma ta alƙawarran da suka sa hannu akai tun ranar 23 ga watan Disamban 2020. ASUU ta ce, in har gwamnatin bata cika sharuɗɗan na ta ba cikin makonni 3 masu zuwa, za ta ɗauki tsattsauran mataki. Har ila yau, ƙungiyar ta kafa kwamiti mai zaman kansa don bincike akan matsayin da aka bai wa ministan sadarwa. Dama…
Read More