15
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanannen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa 'yan bindiga sun ki su daina ta'addanci ne saboda gwamnati ta ki ba su gonaki da kuma "wadatattun kuɗaɗe." Sheikh Gumi ya ce zaman sasanci da aka yi a baya don kawo zaman lafiya tsakanin 'yan bindiga da al'ummar gari ya ciri tura ne saboda rashin biyan su diyya da "gonaki ko shanu ko kuma manyan kuɗaɗen da za su bar aikata wannan ta'asa." Gumi ya bayyana hakan ne a cikin wani karatu nasa da aka sanya kaitsaye a…
