14
Nov
Daga BABANGIDA GORA a Katsina Kimanin mahara sama da ɗari ne su kai dirar mikiya a wata unguwa da ke cikin garin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina. Maharan da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne, da su kai ƙaurin suna a yankin na Batsari da ke makwabtaka da jihar Zamfara da ta daɗe tana fama da masu garkuwa da mutane da satar shanu tsawon lokuta, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Haka zalika maharan sun kai wannan farmaki ne a ranar Talatar da ta gabata da misalin ƙarfe 8:00 na dare, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane…
