NDLEA ta kama hodar ibilis ta biliyan N2 a Abuja

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta cafke wani ɗan Nijeriya mazauni ƙasar Liberia mai safarar miyagun ƙwayoyi, Maduabuchi Chinedu, ɗauke da hodar ibilis mai nauyin kilo giram 9.30 da darajarta ta kai Naira biliyan 2.7 a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Wanda ake zargin wanda ɗan asalin ƙauyen Obaha Okigwe ne da ke ƙaramar hukumar Okigwe a jihar Imo, yana zama a ƙasar Liberia ne a matsayin mai sana’ar haƙar ma’adinai.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya faɗa a ranar Alhamis a Abuja cewa, sun kama wanda ake zargin ne sakamakon binciken haɗin gwiwa da aka aiwatar a kan jirgin ƙasar Ethiopia 911 a filin jirgin sama na Abuja a Larabar da ta gabata inda aka gano hodar sarrafe a cikin kayansa.

Jami’in ya ce yayin biciken farko, Chinedu ya yi iƙirarin cewa ya bar Nijeriya zuwa Liberia ne a 2018 inda a yanzu ya sami izinin zaman ƙasar.

Ya ci gaba da cewa Chinedu ya faɗa musu matsin rayuwa da buƙatar kuɗi don kula da lafiyar mahaifiyarsa ya sanya shi neman taimako a wajen wani abokinsa wanda ke zaune Addis Ababa wanda shi ne ya ba shi aikin safarar hodar zuwa Abuja a kan kuɗi Naira miliyan 1.

Babafemi ya ce da farko an shirya Chinedu ya kai hodar Ivory Coast ne amma daga bisani aka canza tsarin zuwa Nijeriya.

Shugaban NDLEA na ƙasa, Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa (Retd) ya yaba wa duka jami’an da ke da hannu wajen ganowa da kuma kama Chinedu, tare da kira ga jami’an hukumar da su ci gaba da jajircewa a bakin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *