Labarai

Labari da ɗuminsa: Gwamnatin Neja ta haramta acaɓa

Labari da ɗuminsa: Gwamnatin Neja ta haramta acaɓa

A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a jihar Neja, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Abubakar Sani Bello ta kafa dokar haramta acaɓa a faɗin Minna, babban birnin jihar. A cewar Gwamnatin wannan doka za ta soma aiki ne daga ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, 2021. Sai dai sabuwar dokar ta sahale wa masu babura na kansu da su riƙa zirga-zirga daga ƙarfe 6 na safe zuwa 9 na dare. Jihar Neja na daga cikin jihohin da ke matsanancin fama da matsalar 'yan bindiga, domin ko a baya-bayan nan sai da wasu 'yan fashin daji…
Read More
Kisan AIG Dega: Mun kama wasu da ake zargi a Jos – ‘Yan sanda

Kisan AIG Dega: Mun kama wasu da ake zargi a Jos – ‘Yan sanda

Daga AISHA ASAS Rundunar 'Yanan Sandan Nijeriya a Jihar Filato, ta ce ta kama wasu da take zargin suna da hannu a badaƙalar kashe AIG Christopher Dega (mai murabus), kuma mai bai wa Gwamnan Benue, Samuel Ortom, shawara kan sha'anin tsaro. 'Yan bindiga sun kashe tsohon jami'in ɗan sandan ne a Jos babban birnin jihar Filato inda aka yi masa ruwan alburusai a ƙirjinsa wanda nan take rai ya yi halinsa. Kafin ya yi murabus daga aikin ɗan sanda, marigayin ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan 'yan sanda a jihar Barno da Edo. Marigayin ɗan asalin jihar Binuwai ne daga ƙaramar…
Read More
Buhari ya bada odar kuɓutar da ɗaliban Islamiyya 200 da aka sace a Tegina

Buhari ya bada odar kuɓutar da ɗaliban Islamiyya 200 da aka sace a Tegina

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya umarci fannin tsaron ƙasa da ya hanzarta ganowa tare da kuɓutar da ɗaliban Islamiyya su 200 da aka sace a Jihar Neja. Shugaba Buhari ya bada odar hakan ne cikin wata sanarwa da mai magna da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a Abuja a Litinin da ta gabata. A cewar Shehu, Buhari ya yi tir da faruwar lamarin bayan da labari ya isa gare shi. Tare da yin kira ga ɗaukacin hukumomin da lamarin ya shafa da su gaggauta yin abin da ya kamata don kuɓutar da ɗaliban. Haka nan,…
Read More
Ɗaliban Greenfield 14 sun samu ‘yanci

Ɗaliban Greenfield 14 sun samu ‘yanci

An sako ɗalibai 14 na Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka sace daga ɗakunansu na kwana tun a watan Afrilun da ya gabata. Bayanai sun nuna an sako aɗaliban ne a ranar Asabar bayan biyan kuɗin fansar da ba a fayyace ba. Mai Magana da yawun jami’ar, Kator Yengeh, ya tabbatar wa manema labarai da batun sako ɗaliban, tare da cewa nan gaba kaɗan Hukumar Gudanarwar Jami'ar za ta yi ƙarin haske kan lamarin.
Read More
Bagudu ya kama hanyar hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa

Bagudu ya kama hanyar hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa

Daga AISHA ASAS A matsayin wani mataki na hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa a jihar Kebbi da kan yi sanadiyyar hasarar rayuka da dukiyo, gwamnan jihar Atiku Bagudu, ya ce za su duba su yi wa dokokin amfani da kan ruwa na jihar kwaskwarima. Bagudu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Asabar ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha'anin yaɗa labarai, Malam Yahaya Sarki, a Birnin Kebbi. Sanarwar ta nuna Bagudu ya yi wannan bayani ne sa'ilin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Yauri, Dr Muhammad Zayyanu a…
Read More
Almudahana: EFCC ta ƙwato sarƙoƙi na bilyan N14.4 a hannun Diezani

Almudahana: EFCC ta ƙwato sarƙoƙi na bilyan N14.4 a hannun Diezani

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bada bayanin cewa kimar kayan kwalliyar da aka ƙwato daga hannun tsohuwar Ministar Makamashin Fetur, Diezani Alison-Madueke, ya kai Naira bilyan N14.4. Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a Juma'ar da ta gabata a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike kan kayayyakin sata da aka ƙwato, in ji tashar Channels. Bawa ya ce, "Kayan kwalliyar da aka ƙwato a hannun tsohuwar ministar, tsadarsu ya kai Naira biliyan N14.4 kamar yadda hukumomi suka bayyana…
Read More
Lai ga ‘yan Nijeriya: Ƙasa na cikin aminci, babu buƙatar tada hankula

Lai ga ‘yan Nijeriya: Ƙasa na cikin aminci, babu buƙatar tada hankula

Daga WAKILINMU Minista Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bai wa 'yan Nijeriya tabbacin cewa duk da matsalolin tsaron da ƙasa ke fuskanta, Nijeriya na cikin aminci ƙarƙashin gwamnatin Buhari. Da wannan ministan ya yi kira ga 'yan Nijeriya da kada su ji ɗar game da yanayi mara kyau da hasashen masu hasashe ke dangana ƙasar da shi. Lai ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Sarki Adeola Adeniyi Ajakaiye da tawagarsa a Alhamis a ofishinsa da ke Abuja. A cewarsa, "Duk da ƙalubalan tsaron da ake fuskanta, ina so in yi amfani…
Read More
Buhari ya naɗa Yahaya a matsayin magajin Attahiru

Buhari ya naɗa Yahaya a matsayin magajin Attahiru

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya naɗa Major General Farouk Yahaya a matsayin sabon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya. Kafin naɗin nasa, Major General Yahaya babban jami'i ne mai kula da ɓangare na 1 na rundunar sojojin Nijeriya, haka nan shi ne shugaban rundunar shirin Operation HADIN KAI mai yaƙi da ta'addanci a yankin Arewa-maso-gabas. Cikin sanarwar da ya fitar a Alhamis, Daraktan riƙo na sashen labarun rundunar, Brigadier General Onyema Nwachuku, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su yaɗa wannan bayani domin sanar da 'yan ƙasa halin da ake ciki. Da wannan naɗin, ya tabbata cewa Major General…
Read More