Kisan AIG Dega: Mun kama wasu da ake zargi a Jos – ‘Yan sanda

Daga AISHA ASAS

Rundunar ‘Yanan Sandan Nijeriya a Jihar Filato, ta ce ta kama wasu da take zargin suna da hannu a badaƙalar kashe AIG Christopher Dega (mai murabus), kuma mai bai wa Gwamnan Benue, Samuel Ortom, shawara kan sha’anin tsaro.

‘Yan bindiga sun kashe tsohon jami’in ɗan sandan ne a Jos babban birnin jihar Filato inda aka yi masa ruwan alburusai a ƙirjinsa wanda nan take rai ya yi halinsa.

Kafin ya yi murabus daga aikin ɗan sanda, marigayin ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ‘yan sanda a jihar Barno da Edo.

Marigayin ɗan asalin jihar Binuwai ne daga ƙaramar hukumar Katsina Ala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *