27
May
Daga UMAR M. GOMBE Sultan na Sakkwato, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce kada 'yan Nijeriya su yaudari kansu kan cewa lamurra sun daidaita a Nijeriya. Basaraken ya bayyana haka ne a wajen babban taro ka sha'anin tsaron ƙasa a Larabar da ta gabata a Abuja. Sultan ya ce, "Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwan sun daidaita, lamurra sun taɓarɓare. Mun san da haka kuma mun gani. " Wasunmu, mun ga tasku a rayuwa. Yanzu kuwa abubuwa sun yi matuƙar dagulewa. Ba tare da wahalar da tunani ba, za a fahimci cewa Nijeriya na cikin hali mara daɗi kuma gaskiyar kenan."…
