Labarai

Badaƙalar haramta Tiwita: Nijeriya ta gayyaci wakilan Amurka, Birtaniya da Kanada

Badaƙalar haramta Tiwita: Nijeriya ta gayyaci wakilan Amurka, Birtaniya da Kanada

Kimanin sa'o'i 48 da sukar matakin haramta Tiwita da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ɗauka, gwamnatin ta gayyaci wakilan ƙasashen Amurka da Birtaniya da Kanada a Nijeriya da su bayyana a gabanta. Sanarwar gayyatar ta fito ne ta hannun Kimiebi Ebienfa na sashen Sanya Ido Kan Suka da Sadarwa na Ma'aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya. A cewar jami'in, "Biyo bayan haramta Tiwita da Gwamnatin Tarayya ta yi da kuma bayanan da wasu jakadu a Nijeriya suka yi a kan batun dakatarwar, an buƙaci in sanar cewa Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya gayyaci jakadun da lamarin ya shafa zuwa wajen taro…
Read More
Yadda wasu matasan Kano 17 suka rasu a haɗarin mota, Ganduje ya miƙa ta’aziyyarsa

Yadda wasu matasan Kano 17 suka rasu a haɗarin mota, Ganduje ya miƙa ta’aziyyarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu matasa su 17 daga jihar Kano sun rasu sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da su a babbar hanyar Zariya zuwa Kano yayin da suke komawa Kano daga Kaduna bayan halartar ɗaurin auren abokinsu. Wannan mummunan al'amari ya auku ne da yammacin Asabar da ta gabata. Bayanai sun tabbatar cewa wasu daga cikin matasan a nan take suka cika, yayin da wasunsu sai da aka dangana da asibiti kafin rai ya yi halinsa. Majiyar Manhaja ta ce takwas daga cikin marigayan sun fito ne daga yankin Sani Mainagge a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar.…
Read More
Badaƙalar haramta Tiwita a Nijeriya: Sulhu shi ne mafita – Ƙasashen Turai

Badaƙalar haramta Tiwita a Nijeriya: Sulhu shi ne mafita – Ƙasashen Turai

Daga BASHIR ISAH Gwamnatocin Birtaniya (UK), Kanada, Jamhuriyar Ireland, Norway da na Tarayyar Turai (EU) sun yi kira da a tattauna don warware matsalar da ke tsakanin Nijeriya da Tiwita A wani bayanin haɗin gwiwa da suka fitar a Asabar da ta gabata a Abuja aka kuma raba wa manema labarai, ƙasashen sun ce suna goyon bayan 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma damar samun bayanai a matsayin ginshiƙin dimukuraɗiyyar Nijeriya kamar dai yadda lamarin yake a sauran ƙasashen duniya, wannan 'yancin kuwa ya shafi amfani da intanet da kishiyar haka. A cewarsu, "Ɗaukar matakin dakatar da wani al'amari ba…
Read More
Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf ya tallafa wa yara sama da 50 da kuɗin JAMB

Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf ya tallafa wa yara sama da 50 da kuɗin JAMB

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kansilan Guringawa a cikin Ƙaramar Hukumar Kumbotson Jihar Kano ya gabatar wa Babbar Sakatariyar Ilimi ta ƙaramar hukumar Kumbotso da ƙudurin sa na tallafa wa harkar ilimi daga tushe, kana ya gabatar mata da kwamitin da ya kafa na bunƙasa harkar ilimi a mazaɓar sa, wato 'Guringawa Ward Education Promotion Committee', inda kwamitin ya ƙunshi ƙwararrun malaman makarantun firamare, sakandare har zuwa jami'a, sannan da masu hannu da shuni da masu unguwanni da sauran jagororin al'umma har 11 a matsayin mambobin kwamitin. A Alhamis da ta gabata, kwana guda da kai ziyarar kansilan ofishin…
Read More
Haramta Tiwita, Gwamnati ta bada odar hukunta duk wanda aka kama da laifin take doka

Haramta Tiwita, Gwamnati ta bada odar hukunta duk wanda aka kama da laifin take doka

Daga AISHA ASAS Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari'a, Justice Abubakar Malami, SAN ya bada umarnin zartar da hukunci cikin gaggawa a kan duk wanɗanda aka samu da laifin take dokar haramta Tiwita a Nijeriya. Umarnin ministan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar ta hannun hadimin ministan kan sha'anin hulɗa da jama'a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu a ranar Asabar. A cewar sanarwar, "Malami ya bai wa Daraktan Sashen Gabatar da Ƙararraki (DPPF) na ofishinsa, da ya dukufa aiki tare da shirye-shiryen gurfanar da duk waɗanda aka samu sun yi wa dokar Gwamnatin Taryya na dakatar da…
Read More
Labari da ɗuminsa: Kamfanonin sadarwa a Nijeriya sun soma daƙile hanyoyin shiga Tiwita

Labari da ɗuminsa: Kamfanonin sadarwa a Nijeriya sun soma daƙile hanyoyin shiga Tiwita

Da alama dai matakin dakatar da harkokin Tiwita a Nijeriya da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a Juma'ar da ta gabata ya soma aiki. Domin kuwa 'yan Nijeriya sun wayi gari Asabar sun kasa samun zarafin yin mu'amala da shafukan Tiwita kamar yadda suka saba sakamakon kamfanonin sadarwa a ƙasar, da suka haɗa da MTN, Airtel, Glo da kuma 9Mobile, sun soma daƙile hanyar shiga masarrafin Tiwita. Kodayake dai kamfanonin sadarwar ƙarƙashin ƙungiyarsu, sun fito sun bayyana cewa sun soma daƙile hanyar shiga Tiwita ga masu amfani da layukansu kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwa da suka bayar a ranar…
Read More
Gwamnati ta dakatar da harkokin Tiwita a Nijeriya

Gwamnati ta dakatar da harkokin Tiwita a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harkokin kamfanin Tiwita a Nijeriya har sai baba-ta-gani. Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a. Ministan ya nuna yadda ake amfani da shafukan Tiwita wajen aiwatar da harkokin da ke haifar wa Nijeriya cikas. Kazalika, ya ce Gwamnatin Tarayya ta umarci Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Kasa (NBC) da ta hanzarta shirya shirin bada lasisi ga ɗaukacin OTT da kuma harkokin soshiyal midiya a cikin ƙasa. Sanarwar ta fito ne ta hannun hadimi na musamman ga…
Read More
Ranar Keke ta Duniya: FRSC ta shawarci ‘yan Nijeriya su koma amfani da kekuna don rage aukuwar haɗurra

Ranar Keke ta Duniya: FRSC ta shawarci ‘yan Nijeriya su koma amfani da kekuna don rage aukuwar haɗurra

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce amfani da kekuna a matsayin hanyar sufuri zai taimaka wajen rage yawan haɗurra da kuma cinkoson abubuwan hawa a hanyoyi. Shugaban hukumar a jihar Filato, Alphonsus Godwin, shi ne ya bayyana haka a wajen wani gangamin masu tuƙa kekuna da aka shirya a Jos albarkacin Bikin Ranar Keke ta Duniya na 2021. A cewar jami'in, baya ga rage yawan aukuwar haɗurra, haka nan amfani da keke na taimako wajen inganta lafiya da kuma tabbatar da yanayi mai cike da lafiya, don haka ya shawarci al'ummar Filato da kewaye…
Read More
Nagarta: Zulum ya karɓi baƙuncin limamin Ka’aba

Nagarta: Zulum ya karɓi baƙuncin limamin Ka’aba

Daga AISHA ASAS Sakamakon nagartar da gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum ke nunawa a harkar jagorancinsa, ya sanya ɗaya daga cikin limaman Masallacin Ka'aba a Ƙasar Saudiyya, Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, ya ziyarci gwamnan don yabawa da kuma ƙarfafa masa gwiwa. Imam Bukhari, wanda babban malami ne a Jami'ar Ummul Qura da ke Makka, ya ziyarci Barno ne a Larabar da ta gabata inda Gwamna Zulum ya karɓi baƙuncinsa a fadar gwamnatin jihar da ke Maiduguri. Shehun malamin ya yi ziyarar ne bisa gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Al-ansar wadda ke kan gina…
Read More