16
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumomi a Faransa da Switzerland sun kama wasu jiragen sama guda uku na Shugaban ƙasar Nijeriya. Kamen dai ya biyo bayan hukuncin da wata kotu a ƙasar Faransa ta yanke, inda ta bayar da izinin ƙwace jirgin saboda taƙaddamar kasuwanci da ta daɗe ta na yi tsakanin Jihar Ogun da wani kamfanin ƙasar China mai suna Zhongshan. Jiragen da suka haɗa da Dassault Falcon 7ɗ da ke filin tashi da saukar jiragen sama na Paris-Le Bourget da Boeing 737 da Airbus 330 da ke filin jirgin saman Basel-Mulhouse a ƙasar Switzerland an dakatar da…
