25
Oct
Ya umarci su su yi amfani da motoci uku a tawagarsu Ya bayyana haƙiƙanin dalilin korar wasu ministoci Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taƙaita yawan motocin da ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati ke amfani da su a tawagarsu zuwa guda uku, inda ya ce ba za a ƙara wa kowa ba. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce, wannan wani mataki na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka ne na rage kashe kuɗaɗen gwamnati. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya…
