Babban Labari

Abubuwan da zan durfafa a shekarar 2025 – Tinubu

Abubuwan da zan durfafa a shekarar 2025 – Tinubu

*Yadda Shugaba Tinubu ya yi wa ’yan Nijeriya dalla-dalla kan tsare-tsarensaDaga SANI AHMAD GIWA a Abuja A tattaunawar da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ta farko da manema labarai tun bayan ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar a watan Mayun 2023, ya yi wa ’yan Nijeriya tulawar inda gwamnatinsa ta saka gaba, musamman a shekara mai kamawa ta 2025., inda ya ƙara jaddada aniyarsa ta cewa, babu gudu ba ja da baya kan manufofin nasa, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al'umman ƙasar.Yayin da wasu suka bayyana gamsuwa da yadda shugaban ya bayyana manufofinsa, wasu kuwa na ganin…
Read More
Hajji: NAHCON ta cire amfani da Dala

Hajji: NAHCON ta cire amfani da Dala

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da cire amfani da kuɗin Dala wajen biyan kuɗaɗen da suka shafi aikin Hajji, matakin da ya ke da nufin rage tashin gwauron zaɓin kuɗin aikin Hajji. Shugaban Hukumar Na ƙasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya sanar da hakan a yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Sarkin Argungu a fadarsa. Shugaban ya bayyana cewa, biyan muhimman kuɗaɗen ayyukan Hajji, kamar jiragen sama da dala ya taimaka matuƙa wajen tsadar farashin Hajji, wanda hakan ya sa ’yan Nijeriya da dama ba su iya biya. Saleh…
Read More
Abin da Tinubu ke yi da kuɗin tallafi – Idris

Abin da Tinubu ke yi da kuɗin tallafi – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kuɗaɗen da ake samu daga dakatar da biyan tallafin mai ana amfani da su ne wajen aiwatar da ayyuka da tsare-tsare masu tasiri daga Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inji Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na ƙasa, Mohammed Idris. Ayyuka da tsare-tsaren, a cewar Idris, sun haɗa da lamunin ɗalibai, manyan ayyukan zahiri da kuma na zamani, bashi mai rahusa don mabuƙata, inganta harkar noma, da kuma saka hannun jari na zamantakewar ɗan Adam. Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi a taron shekara-shekara na Cibiyar…
Read More
Ba a janye ƙudirin dokar haraji ba – Akpabio

Ba a janye ƙudirin dokar haraji ba – Akpabio

Majalisa za ta bi matakan doka babu tsoro, inji shi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijai ta Nijeriya ta jaddada aniyarta ta ci gaba da bin tsari daki-daki wajen aiwatar da ƙudirin gyaran haraji, inda ta ce, babu wani ɓangare na aikin da aka dakatar ko janye shi. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana a zaman majalisar a ranar Alhamis cewa majalisar ta ci gaba da mayar da hankali kan aikinta na wakiltar muradun ‘yan Nijeriya kuma ba za ta tsorata da matsin lamba daga waje ba. Dangane da batun umarni da shugaban majalisar dattawa, Sanata…
Read More
Za a yi ƙidayar jama’a a 2025 – NPC

Za a yi ƙidayar jama’a a 2025 – NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Alhaji Nasir Isa Kwarra, ya sanar da cewa, za a gudanar da ƙidayar jama’a a Nijeriya a 2025.  Kwarra ya bayyana hakan yayin bikin cika shekara guda na Taron Nairobi kan ƙidaya da Cigaban Al’umma (ICPD) a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, jiya Alhamis.  Duk da shawarar Majalisar ɗinkin Duniya na cewa, a gudanar da ƙidaya duk bayan shekaru 10, Nijeriya ta yi ƙidayar ƙarshe ne a 2006.  Gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ta gabata ta ɗage ƙidayar a 2023, inda ta nemi gwamnatin da…
Read More
Tsakanin ƙudirin dokar haraji da rayuwar talakan Nijeriya

Tsakanin ƙudirin dokar haraji da rayuwar talakan Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Makonni bayan miƙa wasu ƙudurori huɗu da ke da nufin yin garambawul ga tsarin harajin Nijeriya ga majalisar mokokin ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya yi, har yanzu wannan batu na ci gaba da haifar da cecekuce a majalisar da ma ɓangarorin ƙasar baki ɗaya game da manufar waɗannan ƙudirorin. Wasu dai sun bayyana fargabar cewa ƙudurorin na iya jawo ƙarin haraji ta yadda za su ƙara ɗora wa 'yan ƙasar nauyi. Ra’ayoyin 'yan Nijeriya dai sun bambanta kan wannan lamari, inda da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan abin da wannan ƙuduri ke…
Read More
Lakurawa: Daga sojojin haya zuwa ‘yan ta’adda

Lakurawa: Daga sojojin haya zuwa ‘yan ta’adda

Asalin Lakurawa da alaƙarsu Al-qa'eda Gaskiyar magana kan harin Mera da abinda ya biyo baya Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja da JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Lakurawa, kamar yadda ake kiran ayarin waɗansu mutane da ke da'awar Musulunci tsantsa da suke da sansanoni akan iyakokin Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar tun daga yankunan ƙananan hukumomin Arewa da Augie da ke Jihar Kebbi zuwa ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza da Silame da Kware da Gwadabawa zuwa Illela da ke Jihar Sokoto, mutanen da ke zaune a waɗannan yankunan sun daɗe suna ganin waɗannan mutanen ɗauke da makamai suna shiga garuruwansu…
Read More
Ƙungiyar ta’addanci ta Lukarawa ta ɓullo – Hedikwatar Tsaro

Ƙungiyar ta’addanci ta Lukarawa ta ɓullo – Hedikwatar Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta tabbatar da ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci da aka fi sani da Lukarawa a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis a Abuja. Janar Buba ya bayyana cewa, sabuwar ƙungiyar ta'addancin ta samo asali ne daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan, wanda ya kawo cikas ga haɗin gwiwar…
Read More
VAT: Ku mayar da wuƙar – Gwamnati ga ‘yan Arewa

VAT: Ku mayar da wuƙar – Gwamnati ga ‘yan Arewa

Ba don kassara Arewa ba ne, a cewar fadar Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa ta buƙaci Tinubu ya janye ƙudirin Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta ce saɓanin fargabar rasa ayyukan yi da kuma ganin cewa an mayar da yankin Arewa saniyar ware, ƙudirin sake fasalin harajin da ke gaban majalisar dokokin ƙasar zai amfanar da dukkanin jihohin ƙasar nan da kuma daidaita dokokin harajin ƙasar domin su inganta. Ya ce ya zama wajibi a magance rashin fahimtar juna a kan batun sake fasalin haraji da gwamnatin ta fara aiwatarwa bayan wani taro da gwamnonin Arewa suka…
Read More
Tinubu ya tsuke wa ministocinsa bakin aljihu

Tinubu ya tsuke wa ministocinsa bakin aljihu

Ya umarci su su yi amfani da motoci uku a tawagarsu Ya bayyana haƙiƙanin dalilin korar wasu ministoci Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taƙaita yawan motocin da ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati ke amfani da su a tawagarsu zuwa guda uku, inda ya ce ba za a ƙara wa kowa ba. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce, wannan wani mataki na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka ne na rage kashe kuɗaɗen gwamnati. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya…
Read More