Babban Labari

Gwamnati ta dakatar da jirgin Air Nigeria har sai baba-ta-gani

Gwamnati ta dakatar da jirgin Air Nigeria har sai baba-ta-gani

Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar cewa, ta dakatar da aikin kamfanin jirgin saman Nijeriya, wato Air Nigeria. Sanarwar wadda aka fitar a ranar Litinin ta ce, dakatarwar ta har baba-ta-gani ce. Ministan Sufurin Jirgin Sama, Festus Keyamo, shi ne ya bayyana haka yayin da yake ba da bayani kan ayyukan ma'aikatarsa a matsayin ɓangare na cika Shuga Bola Tinubu shekara guda a ofis. Da yake ƙarin haske kan dalilin dakatarwar, Keyamo ya ce, jirgin da aka nuna cewa ta Nijeriya ne ba gaskiya, rufa-rufa ce kawai aka yi wa lyan ƙasa a wancan lokaci.
Read More
An maka gwamnonin Nijeriya a kotu kan rashin sakar wa ƙananan hukumomi mara

An maka gwamnonin Nijeriya a kotu kan rashin sakar wa ƙananan hukumomi mara

Gwamnatin Tarayya ta maka Gwamoni 36 na Jihohin Nijeriya a Kotun Ƙoli kan tauye haƙƙoƙin Shugabannin Ƙananan Hukumomi. Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi ne ya tabbatar da hakan. Lateef ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙwato wa shugabannin ƙananan hukumomi 'yancinsu a hannun gwmanoni, tare da ba su cikakken ikon cin gashin kansu. Kazalika, Gwamnatin ta kuma buƙaci Kotu da ta bayar da umarnin haramta wa gwamnoni sauke zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi ba bisa ƙa'ida ba. Ta kuma buƙaci Kotun ta ba damar da za a tiƙa tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗen kai-tsaye daga asusun…
Read More
Yanzu-yanzu: Abba ya ba da umarnin kama tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Yanzu-yanzu: Abba ya ba da umarnin kama tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin gaggawa kan a tsare tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero. News Point Nigeria ta rawaito cewar, Mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi ne ya shaida wa manema labarai hakan da safiyar Asabar. A cewar Yusuf, ‘Komawar Aminu Ado Bayero Kano ba komai ba ne face haddasa rashin lumana a jihar'. “Don haka na bai wa Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar umarnin ya kama Alhaji Aminu Ado Bayero, a duk inda ya gan shi a jihar," in ji sanarwar.
Read More
Sanusi ya dawo!

Sanusi ya dawo!

…kan karagar Sarkin Kano…Mun ba tsoffafin sarakuna kwanaki biyu su kwashe komatsansu – Gwamna Abba Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana Muhammadu Sanusi ll, wanda aka fi sani da Sanusi Lamiɗo Sanusi, a matsayin sabon Sarkin Kano na 16 da zai cigaba da zama karagar mulkin Masarautar Kano. Gwamna ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da ya ke rattaɓa hannu kan dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore, ta yi wa gyara ta shekarar 2019. Haka kuma Abba Kabir ya ce,…
Read More
Babu sarki a Kano a halin yanzu — Majalisa

Babu sarki a Kano a halin yanzu — Majalisa

Biyo bayan soke masarautun da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta ƙirƙiro a Kano a zaman da ta yi ranar Alhamis, Majalisar Dokokin Jihar ta ce a halin yanzu babu sarki a Kano. Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske dangane da matakin rushe masarautun da majalisar ta ɗauka. Ya ce a halin da ake ciki an aike da dokar masarautun da aka yi wa kwaskwarima ga Gwnan Kano, Abba Kabir, don ya rattaɓa hannu. Ya kara da cewa, dokar ta bai wa Gwamna…
Read More
Yanzu-yanzu: Kotu ta ba da belin Abba Kyari

Yanzu-yanzu: Kotu ta ba da belin Abba Kyari

A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin DCP Abba Kyari, na mako biyu. Kotu ta ba da belin ne don bai wa Kyari damar zuwa kammala jana'izar mahaifiyarsa da ta rasu. Kazalika, Kotun ta tsayar da ranar Juma'a, 31 ga Mayu a matsayin ranar da za ta yi matsaya kan buƙatar belin da Kyari ya gabatar mata. Idan ba a manta ba, Kyari na fuskantar shari'a ne kan tuhume-tuhume masu nasaba da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi daga hukumar NDLEA.
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarautu kwaskwarima bayan shan kiraye-kiraye kan a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi, wanda tsohuwar gwamnatin Umar Ganduje ta tsige. Majalisar ta yanke shawarar yi wa dokar kwaskwarima ne bayan da Shugaban Masu Rinjaye, Hussien Dala, mai wakiltar Mazaɓar Dala, ya miƙa ƙorafinsa yayin zaman majalisar a ranar Talata. An fara yi wa wannan doka kwaskwarima ne a 2019 bayan da ruwa ya yi tsami tsakanin gwamnan jihar na wancan loakci, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano na 14, Sunusi. Sakamakon gayaran da aka yi wa dokar a…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a Filato

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a Filato

Bayanan da suka iso mana yanzu daga jihar Filato sun ce, 'yan bindiga sun kai ƙazamin hari ƙauyen Zurak da ke Gundumar Bashar District cikin ƙaramar hukumar Wase, Jihar Filato, inda suka kashe sama da mutum 40. A cewar mazauna yankin lamarin ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 5 na yamma yayin da jama'a ke gudanar da harkokinsu. Sun ƙara da cewa, ba su samau damar sanar da abin da ya auku d wuri ba ne sakamakon rashin kyawun sabis a yankin. Wani shugaban matasan yankin mai suna Sahpi’i Sambo, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar Daily…
Read More
Adadin waɗanda suka rasu a harin masallaci a Kano ya ƙaru zuwa 15

Adadin waɗanda suka rasu a harin masallaci a Kano ya ƙaru zuwa 15

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin da wani matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci a Kano ya kai mutum 15, Ana zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare da mutum kusan 40 a ciki. Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado, Shafi’u Abubakar ya yi zargin mutanen da ya cinna wa wutar mafi yawancinsu suna cikin Masallacin kuma sun cutar da shi a rabon gadon, Tuni…
Read More