Babban Labari

Yanayin kasuwa ya haifar da ƙarin farashin fetur – Kyari

Yanayin kasuwa ya haifar da ƙarin farashin fetur – Kyari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kamfanin Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce yanayin kasuwa ne ya haifar da ƙarin farashin fetur da aka fuskanta a ranar Talata. Kyari ya bayyana haka ne yayin ganawarsu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya ce sakar wa ɓangaren mai mara da aka yi, hakan zai sa a riƙa fuskantar hawa da saukar farashin man lokaci-lokaci. Shugaban na NNPCL ya ce batun ƙarin farashin fetur daga N540 zuwa N617 da aka fuskanta ba wai don ƙarancin fetur ba ne, tare da tabbatar wa 'yan…
Read More
An ƙara kuɗin fetur a Nijeriya

An ƙara kuɗin fetur a Nijeriya

A halin da ake ciki, 'yan kasuwa sun cilla farashin fetur daga N537 zuwa N617 kan lita guda a wasu gidajen mai mallakar Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL). An ga wani gidan mai mallakar NNPC s ranar Talata a Abuja yana sayar da fetur N617 kan kowace lita. Ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren NNPC ko makamancin haka dangane da ƙarin kuɗin man. Tun bayan da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai baki ɗaya a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki a watan Mayu, farashin man ya cilla sama…
Read More
Shugabancin APC: Kyari ya maye gurbin Adamu

Shugabancin APC: Kyari ya maye gurbin Adamu

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shuagaban Jam'iyyar APC na ƙasa da daga shiyyar Arewa, Abubakar Kyari, ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa biyo bayan murabus da Adamu ɗin ya yi. Wannan sauyin da jam'iyyar ta APC ta samu ya yi daidai da tanadin kundin dokokin jam'iyyar, wanda ya nuna cewa idan shugaban jam'iyyar na ƙasa ya yi murabus mataimakinsa ya maye gurbinsa a matsayin riƙon ƙwarya. An ga Kyari ya jagoranci mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam'iyyar wajen yin taro a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja cikin tsattsauran tsaro a ranar Litinin.…
Read More
Adamu ya yi murabus daga shugabancin Jam’iyyar APC

Adamu ya yi murabus daga shugabancin Jam’iyyar APC

Daga BASHIR ISAH Sbugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya miƙa wasiƙar yin murabus daga kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar kamar yadda Jaridar News Point Nigeria ta rawaito. Majiyar News Point Nigeria ta bayya cewar, Sanata Adamu wanda ya zama shugaban APC a watan Maris, 2022, ya miƙa wasiƙar murabus daga muƙaminsa ga Fadar Shugaban Ƙasa gabanin dawowar Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga taron Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) da ya halarta a ƙasar Kenya. Majiyar jaridar ta ce, Adamu ya aike da wasiƙar tasa ce ga Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da misalin ƙarfe 4 na yammacin…
Read More
Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin sabbin hafsoshin tsaro

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin sabbin hafsoshin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da naɗin shugabannin hukumomin tsaro, waɗanda sabon Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa. Majalisar Dattawa Nijeriya ta tabbatar da sunayen mutanen a ranar Alhamis, 13 ga Yuli, 2023, bayan tantance su a wani zaman sirri da aka kwashe sama da awa ɗaya ana yi. Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya ce yayin zaman sirrin, shugabannin hafsoshin sun amsa tambayoyi kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma batutuwan da suka jivanci hakan. Shugaban ƙasar a cikin wata wasiƙa da aka karanta a ranar Litinin a zauren majalisar ya…
Read More
Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Daga NAISR S. GWANGWAZO a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa, ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, a gaban kotu. Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin da ta ke mayar da martani kan hukuncin umarnin Babbar Kotun Abuja, wacce ta umarci hukumar da ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin mako guda ko kuma ta sake shi nan take. A yayin da Mai Shari’a Hamza Mu’azu ke yanke hukuncin kan haƙƙin bil’adama a ranar Alhamis, ya ce, cigaba da tsare mutum komai gajeren lokaci ya saɓa da haƙƙin…
Read More
An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

An zaɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). Wannan ya faru ne yayin taron ƙungiyar karo na 63 wanda ya gudana a Guinea Bissau a ranar Lahadi. Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023. A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Legas, inda ya ce sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.” A wancan lokacin, Tinubu ya ce…
Read More
Tinubu bai fitar da jerin sunayen ministoci ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu bai fitar da jerin sunayen ministoci ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Alhamis Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, ba a kammala shirya jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai naɗa ba. Mataimakin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja. Alake ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da jita-jitar da ke tattare da jerin sunayen ministocin da ake jira. "Game da jerin ministocin, babu gaskiya a cikin duk waɗannan abubuwan," inji Alake. "Lokacin da Shugaban Ƙasa ya natsu…
Read More
Ba zan wahalar da ’yan Nijeriya kamar gwamnatin Buhari ba – Tinubu

Ba zan wahalar da ’yan Nijeriya kamar gwamnatin Buhari ba – Tinubu

*Ya rage harajin da aka ƙaƙaba na shigo da motoci da sauransu  Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sauya wasu harajin da aka sanya a cikin mintunan ƙarshe da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rattava wa hannu, yana mai cewa ba zai shaƙe ‘yan Nijeriya ya wahalar da su kamar yadda gwamnatin baya ta yi ba. Shugaban ya soke harajin ne a cikin umarnin zartarwa a jiya Alhamis, 6 ga Yuli, 2023. Harajin sun haɗa da dakatar da harajin kashi 5 da ake cece-kuce kan ayyukan sadarwa; Harajin Kore na kashi 10…
Read More
Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH 'Yan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da Peter Obi na Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya gabata, sun yi ca a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ƙin yarda da rahoton ƙarshe da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata. A ranar Talata, 27 ga Yuni, EU ta miƙa rahoton nata game da zaɓen a Abuja. Babban jami'in sanya ido, Barry Andrews, ya ce rahoton ya samo asali ne daga nazarin bin ƙa’idojin da Nijeriya ta ɗauka na…
Read More