29
Apr
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya jaddada cewa matakin cire tallafin fetur da gwamnatinsa ta ɗauka abu ne da ya zama wajibi don hana ƙasar faɗawa cikin fatara. Tinubu ya bayyana haka a ne sa'ilin da yake jawabi a wajen taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya a ranar Lahadi. Ya ce akwai buƙatar cire tallafin na fetur domin sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar. Ta bakinsa, “Ga Nijeriya, mun yi amannar haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗa kai ya zama dole don samar da kwanciyar hankali a sauran ƙasashen duniya. "Game…
