Babban Labari

Gabanin zaɓen shugabannin majalisa… A na zargin ƙulla maƙarƙashiyar kama Yari

Gabanin zaɓen shugabannin majalisa… A na zargin ƙulla maƙarƙashiyar kama Yari

*Ƙungiya ta ja hankalin Tinubu da APC*Kotu ta tsawaita wa’adin hana kama shi*Za a ƙaddamar da Majalisa ta 10 ranar Talata Daga NASIR S. GWANGWAZO da MAHDI M. MUH’D Rahotanni sun nuna cewa, jami’an tsaron Nijeriya suna ƙulle-ƙullen kama tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, su tsare shi har sai bayan ƙaddamar da Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 da za a yi ranar Talata mai zuwa, don tabbatar da cewa, bai samu damu tsaya wa takarar shugabancin Majalisar Dattawa ba. Wannan zargin ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar Matasan Yankin Arewa Maso Gabas (North East Youth Organisation Forum), Alhaji…
Read More
Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Daga BASHIR ISAH Gwamnoni 36 a faɗin ƙasa, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da batun cire taffin mai. Gwamnonin sun bayyana haka ne yayin ganawar da Shugaban Ƙasar ya yi da Ƙungiyar Gwamnoni (NGF), ranar Laraba a fadarsa da ke a Abuja. Gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, sun bayyana farin ciki da gamsuwarsu game da matakin cire tallafin mai da Shugaba Bola ya ɗauka. Kazalika, sun bai wa Tinubun tabbaci tare da ɗaukar masa alƙawarin za su yi aiki tare a kan haka. Tun farko da yake jawabi, Shugaba Tinubu ya…
Read More
Batun cire tallafin mai ya rikita ƙasa

Batun cire tallafin mai ya rikita ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tun bayan da zaɓaɓɓen sabon Shugaban Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya furta kalaman cewa, an kawo ƙarshen biyan tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ke yi a ƙasar, al’amura suka soma rikicewa, inda kace-nace ya ɓalle kan batun, sannan kayayyaki suka yi mummunan tashin gwauron zabo, wanda ba a tava ganin irinsa ba a nan kusa, musamman ma farashin litar man fetur ya ninka kusan sau uku. Shugaba Tinubu ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa na farko a matsayin Shugaban Ƙasa ranar Litinin, 29 ga Mayu,…
Read More
Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga sassan Nijeriya sun ce, a halin da ake ciki farashin fetur ya ƙaru zuwa Naira 700 kan kowace lita a wasu sassan ƙasar. Wannan ya biyo bayan sanar da cire tallafin mai baki ɗaya da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawbinsa ga ‘yan ƙasa jim kaɗan da rantsar da shi a ranar Litinin da ta gabata. Binciken Manhaja ya gano cewar, matakin cire tallafin da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya haifar da ƙarin farashin mai da kashi 100 zuwa 250, inda a yanzu ake sayar da lita guda na fetur tsakanin…
Read More
Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Da alama layukan ababen hawa a gidajen mai ya dawo a Jihar Legas sa'o'i bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai. Bayanai sun ce an ga cinkoson ababen hawa a gidajen mai ɗin NNPC a yankunan Ikeja da Alausa waɗanda ke jiran su sha mai. Ya zuwa haɗa wannan labari, an ga da daman gidan mai masu zaman kansu a yankunan ba su sayar da mai. A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce masu ƙumbar susa kaɗai ke amfna da tallafin mai amma ban da talakawa. Ya ce, “Mun yaba da ƙoƙarin gwamnati mai barin gado…
Read More
Buhari da Tinubu: Ta faru ta ƙare!

Buhari da Tinubu: Ta faru ta ƙare!

*Yayin da Tinubu ya kammala shirin amsar mulki…*Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗe 33 kwanaki shida kafin miƙa mulki*Dalilin da ya sa Buhari ke ta ɗaukar matakai – Fadar Shugaban Ƙasa *Ana shirin kawo cikas ga bukukuwan miƙa mulki a jihohi da ƙasa, inji DSS*Sa'o'i kafin miqa mulki Buhari ya umarci ministocinsa su cigaba da aikinsu*Ƙananan ministoci ba su da amfani a gwamnatin Buhari – Keyamo Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin sabon Shugaban Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, za ta fara aiki a matsayin halastacciyar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula, yayin da…
Read More
Za a jinginar da filayen jirgin saman Kano da Abuja

Za a jinginar da filayen jirgin saman Kano da Abuja

*Za a ƙara ciwo bashin Dala miliyan 800*Za a nutsar da kuɗin a shirin rage raɗaɗin cire tallafin fetur Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Malam Aminu Kano da ke Kano. Gwamnati ta amince da wannan mataki ne a taron majalisar koli da aka gudanar ranar Laraba a Abuja. Ministan Sufirin Jiragen Sama a Nijeriya, Hadi Sirika, ya shaida wa BBC cewa za a jinginar da filin jirgin Abuja na shekara 20, sannan na Kano na tsawon shekara 30. Sirika ya ce taron…
Read More
Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karɓar bashin N368bn daga Bankin Duniya

Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karɓar bashin N368bn daga Bankin Duniya

Majalisar Tarayya ta Ƙasa ta amince wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya kinkimo bashin Naira biliyan 368.7 (Dala miliyan 800) daga Bankin Duniya. Mamba a Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sha'anin Bashi da Tallafi, Abubakar Yunusa Ahmad, shi ne ya bayyana haka a wani shiri da Tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Juma'a. Sai dan majalisar ya ce ba za a yi amfani da bashin ba a gwamnatin Buhari mai ƙarewa. Yana mai cewa, gwamnati mai jiran gado ce za ta sarrafa bashin don cimma manufar da ta sa aka ciyo shi. A cewarsa, game da Dala…
Read More
Tinubu ya gana da Kwankwaso a Faransa

Tinubu ya gana da Kwankwaso a Faransa

Daga BASHIR ISAH Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a Paris, babban birnin ƙasar Faransa. Bayanai sun ce Tinubu da Kwankwaso sun yi ganawar sirri bayan haɗuwar tasu inda suka shafe sa'o'i huɗu suna tattaunawa. Majiyarmu ta ce tattaunawar tasu ta shafi yadda za a yi tafiya tare da Kwankwaso a gwamnati mai jiran gado kasancewar Tinubu na da ra'ayin kafa gwamnati ta haɗin kan ƙasa. Kazalika, majiyar ta ce daga cikin batutuwan da suka tattauna har da batun shugabancin majalisar tarayya. Wadanda suka halarci…
Read More