Babban Labari

Almudahanar N2.1bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina

Almudahanar N2.1bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina

*Maina zai shafe shekara takwas a gidan kaso Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara takwas da aka yanke wa tsohon Shugaban Kwamitin Kula da Fansho, Abdulrasheed Maina kan yin sama-da-faɗi da kuɗaɗen fansho Naira biliyan 2.1. Alƙalan da suka saurari shari'ar, baki ɗaya su ukun sun yi ittifaƙi kan tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina kamar yadda Mai Shari'a Okon Abang ya karanto. Jagoran alƙalan, Elfreda Williams-Daudu, ya tabbatar da hukuncin da Babbar Kotu ta yanke wa Maina ɗin wanda a kan haka shi Maina ya ɗaukaka ƙara. Alƙalin ya ce an…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara

Rahotanni daga jihohin Zamfara da Kebbi sun ce 'yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 40 a ƙauyukan jihohin yayin harin da suka kai da asubahin ranar Lahadi. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, wasu 'yan sanda guda shida na daga cikin mutum 36 da 'yan bindigar suka kashe a Ɗan Umaru da ke yankin Zuru a Jihar Kebbi. Mazauna yankin sun ce an yi jana'izar mutum 27, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin. Kazalika, sun ce 'yan bindigar sun sace mutane da dama haɗi da shanun jama'a yayin harin da suka kai ƙauyuka maƙwafta. Bayanai sun ce maharan…
Read More
Mun gyara aikin soja a Nijeriya – Shugaba Buhari

Mun gyara aikin soja a Nijeriya – Shugaba Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, an cimma ƙwararan shirin inganta tsaro a Nijeriya, tare da inganta kayan aiki, horar da jami’ai da tsarin jin daɗin jama’a da ya shafi fiye da yara 50,000 na jaruman sojojin da suka mutu. Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, a wani bikin da ya samu halartar tsaffin shugabannin ƙasar biyu, shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon da shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, shugaban ƙasar ya ce, ya kafa aikin ɗaukar sojoji 60,000 a aikin soja, kuma dubbai aka yaye daga makarantar horar da sojoji ta Nijeriya da sauran cibiyoyin…
Read More
An dakatar da cire tallafin fetur a Nijeriya

An dakatar da cire tallafin fetur a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ƙarshe dai, Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar tsawaita wa’adin cire tallafin man fetur har bayan wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari a karagar mulki. Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wannan Alhamis yayin da ta ke zantawa da manema labarai a Abuja. A cewarta, Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa NEC ce ta yanke shawarar cewa ba yanzu ne lokacin da ya dace a cire tallafin man fetur ba a ƙasar. Ministar wadda ta bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ta ce…
Read More
Tinubu ya miƙa wa Buhari hannayen amsar mulki

Tinubu ya miƙa wa Buhari hannayen amsar mulki

*Tinubu ya bada sunayen mutane 13*Buhari ya ɓaro manyan ayyukan Naira tiriliyan 1.535*Buhari zai gadar wa Tinubu shirin maganta matsalar tsaro na shekara biyar Daga SANI AHMAD GIWa da MAHDI M. MUHAMMAD Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Boss Mustapha sunayen mutane 13 da za su yi aiki da kwamitin miƙa mulki da bangaren gwamnati mai barin gado da take ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari. Tinubu ya kasance a ranar 1 ga Maris, 2023, aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 ga…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Gobe take Ƙaramar Sallah a Nijeriya

Da Ɗumi-Ɗumi: Gobe take Ƙaramar Sallah a Nijeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa ya samu sahihan rahotanni daga sassan ƙasa dangane da ganin watan Ƙaramar Sallah. Don haka idan Allah Ya kai mu gobe Juma'a, take 1 ga watan Shawwal, 1444 AH wanda ya zo daidai da 20 ga Afrilu, 2023. Kwamitin tantance ganin wata ƙarƙashin jagorancin Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan.
Read More
Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

*Ta ba da umarnin dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe Babban Ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ya dakatar ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen cike giɓi na Gwamnan Jihar Adamawa da ya gudana ranar Asabar. Ofishin ya ɗauki wannan mataki ne bayan da labarin ayyana 'yar takarar Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓe da Kwamishinan Zaɓe na jihar, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya yi a ranar Lahadi ya isa gare shi. Cikin sanarwar da INEC ta wallafa a shafinta na Tiwita mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan hukumar, Barista Festus…
Read More
Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa. Kwamshinan Zaɓe na Jihar Adamwa, Farfesa Hudu Yunus Ari, shi ne ya bayyana nasarar Binani wadda ta kasance 'yar takarar Jam'iyyar APC. Da fari, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam'iyyar PDP ne ke gaba da yawan ƙuri'u kafin daga bisani Binani ta shige gabansa. Magoya bayan jam'iyyar PDP sun nuna rashin jin daɗinsu ganin Kwamishinan Zaɓe na jihar ne ya bayyana sakamakon zaɓen maimakon Baturen Zaɓe. Da wannan nasarar da ta samu, a iya cewa Sanata Aisha ta zamo mace ta…
Read More
Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin sake zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a gobe, 15 ga Afrilu, 2023, jam’iyyun adawa da ’yan takara, a ƙarshen mako, sun ƙara zage damtse don samun galaba a zaɓen da kuma rage ƙarfin jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dokokin Ƙasa. Za a cike zaɓen gwamnoni biyu, na sanatoci biyar, na majalisar wakilai 31 da kuma kujeru 57 na jiha. Jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da na 18 ga watan Maris, inda…
Read More
Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

*Ya roƙi ga ɗan takarar na PDP*Dalilan da suka hana Atiku cin zaɓe, inji Tinubu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a kodayaushe yana shan kayi a yunƙurinsa na neman shugabancin Nijeriya tun shekarar 1993. Don haka sai Tinubu ya roqi Atiku da kada ya kalli rashin nasararsa a zaɓen da ya gabata a matsayin baƙon abu, yana mai cewa, hakan ba zai zama abin al’ajabi ga Jam’iyyar PDP da ɗan takararta idan aka yi la’akari da rikicin da…
Read More