Babban Labari

Da Ɗumi-ɗumi: Kano ta zama ta Abba Yusuf

Da Ɗumi-ɗumi: Kano ta zama ta Abba Yusuf

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe INEC, ta tabbatar da ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar NNPP a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Abba ya taki wannan matsayi ne bayan da ya samu ƙuri'u 1,019,602 wanda hakan ya ba shi damar doke babban abokin hamayyarsa na APC kuma Mataimakin Gwamnan jihar mai ci, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya tsira da ƙuri'u 890,705 a zaɓen. INEC ta ce Muhammad Sani Abacha na Jam'iyyar PDP, shi ne ya zo na uku da ƙuri'u 15,957. Da safiyar wannan Litinin INEC ta ayyana Abba sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Kano…
Read More
Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bayan haƙuri a kan layi na tsawon lokaci, gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauke nayinsa na jama'a a mazaɓarsa na PU024 da ke Unguwar Sarki GRA a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa. Da yake magana da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, El-Rufai ya ce, ana neman masu kaɗa ƙuri’a a yankin Kudancin Kaduna da su zaɓi wata jam’iyya ko kuma su koma gidajensu. Ya ce, a halin yanzu jami’an tsaro na gudanar da bincike a jihar. Gwamnan ya ce, an gudanar da zaɓen a wasu rumfunan zaɓe ba tare da wata matsala ba. “Babu komai,…
Read More
Zaɓen gwamnoni: A ina za a iya yin ‘inconclusive’ bana?

Zaɓen gwamnoni: A ina za a iya yin ‘inconclusive’ bana?

*Ba a san maci tuwa ba..! Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gobe ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki na jihohi a Tarayyar Nijeriya, waɗanda ake sa ran rantsarwa a ranar 29 ga Mayu, 2023, bayan kammala wa’adin zangon gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihohi. Zaɓen da ya gabata na 2019 ya zo da wani sabon salon ƙa’idar da ba a saba gani ba a zaɓukan baya, inda ba a sanar da sakamakon zaɓe bisa dalilin wata kalma ta ‘inconclusive’, wacce ta ke nufin ‘rashin kammaluwa’ ko kuma ‘zaɓen da bai kammalu ba’. Shin mene ne…
Read More
Gwamnati ta daƙile kutse ta yanar gizo sau miliyan 12.9 lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa – Pantami

Gwamnati ta daƙile kutse ta yanar gizo sau miliyan 12.9 lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa – Pantami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ta bayyana cewa an samu jimillar hare-hare 12,988,978 da suka samo asali daga ciki da wajen Nijeriya a lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gudana 25 ga Fabrairu, 2023. A cewar Pantami, a kullum ana samun barazanar da bai gaza 1,550,000 ta yanar gizo da kafofin sadarwa, inda ya ƙara da cewa alƙaluma daga bisani suka haura zuwa 6,997,277 a ranar zaɓen Shugaban Ƙasa. Wata sanarwa a ranar Talata ta bakin mai magana da yawun Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na…
Read More
CBN ya bai wa bankuna odar ci gaba da karɓar tsoffin kuɗi

CBN ya bai wa bankuna odar ci gaba da karɓar tsoffin kuɗi

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ba da umarnin bankuna su ci gaba da karɓa da kuma ba da tsoffin tarkadun kuɗi na N200 da N500 da N1000 har zuwa 31 ga Disamban 2023. CBN ya amince da hakan ne domin cika umarnin Kotun Ƙoli biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke ran 3 Maris inda ta buƙaci da a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin har zuwa ƙarshen wannan shekarar. Muƙaddashin Daraktan Sadarwa na bankin, Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyna amincewar CBN na ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin a sanarwar da ya fitar…
Read More
Dalilina na ƙin karɓar takardar shaidar cin zaɓe a NNPP – Sanata Shekarau

Dalilina na ƙin karɓar takardar shaidar cin zaɓe a NNPP – Sanata Shekarau

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilinsa na ƙaurace wa taron miƙa wa  zaɓaɓɓun sanatoci takardar shaidar lashe zaɓen da aka gudanar a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, a makon nan. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Malam Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a ƙarƙashin jtsohuwar jam’iyyarsa ta NNPP maimakon jam’iyyarsa ta yanzu, PDP. Sai dai ɗan majalisar mai ci bai halarci taron miqa takardar shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun sanatocin ba a ranar Talatar da ta gabata.…
Read More
Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani yanayi mai nuna alamun kutingwila ga lashe zaɓen 2023 da zavavven Shugaban Ƙasa mai jiran gado a Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi, wasu ’yan Nijeriya da dama mazauna Birnin Landon, Babban Birnin Ƙasar Ingila, sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar dake birnin Landan ɗin na ƙasar Birtaniya. Wannan ya faru ne jim kaɗan bayan Chatham House ya soki lamarin yadda aka tattara sakamakon zaɓen, wanda ya bai wa Tinubun nasara, inda gidan na dimukraɗiyya ya ce, ba a bi qa’idojin zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman…
Read More
Ɗan Chana ya fallasa abubuwan ta’ajibi a shari’ar kisan Ummita

Ɗan Chana ya fallasa abubuwan ta’ajibi a shari’ar kisan Ummita

*Ba na roƙon kada a kashe ni, inji shi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan ƙasar Chana ɗin nan mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe masoyiyarsa, jiya Alhamis ya sake faɗa wa kotu a Kano cewa bai taɓa niyyar kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ummukulsum Sani 'yar shekara 22, da aka fi sani da Ummita ba. Wanda ake tuhumar, mazaunin Railway Quarters a Kano, ana tuhumar sa da laifin kisan kai. Da lauyan gwamnati, Musa Lawal ke tambayar dalilin sa na zuwa gidan su Ummita ba tare da gayyata ba,…
Read More
Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Daga WAKILINMU Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana yadda aka tilasta masa tafka maguɗi a sakamakon zaɓe a matsayinsa na Baturen Zaɓe a yankin Tudun Wadah, Kano, yayin zaɓen da ya gudana. Cikin wasiƙar da ya aika wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Ibrahim Yakasai ya aibata sakamakon zaɓen da ya bayyana bayan kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya. A cewarsa, tilasta masa aka yi kan ya tafka maguɗin zaɓe bayan da aka jefa rayuwarsa cikin haɗari a zahiri. Ya ce galibin sakamakon zaɓen da jami’an zaɓe suka bayyana ba na…
Read More