Ba jami’an CPG suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada ba – Gwamnatin Zamfara

*An kama waɗanda ake zargi

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla ‘yan banga 10 ne aka tsare bisa zargin kisan malamin addini a Jihar Zamfara.

MANHAJA ta rawaito an kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada ne a ranar Talata a garin Mada da ke cikin yankin Ƙaramar Hukumar Gusau a jihar.

Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya ce waɗanda hukuma ta kama ‘yan banga ne ba jami’an bai wa al’umma kariya (CPG) ba.

MANHAJA ta rawaito ana zargin jami’an CPG da yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada kisan gilla, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin ruɗani.

Sai dai sanarwar da Sulaiman ya fitar a ranar Laraba ta nuna cewa, ‘yan bangan da aka kama ɗin ba su da sahalewar gudanar da ayyukan tsaro daga gwamnatin jihar.

Ta ce, “Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu mummunan labari game da kisan gillar da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada.

“Jami’an tsaro sun samu nasarar damƙe baki ɗayan ‘yan bangan da ake zargi da hannu a kisan.

“Gwamnatin Zamfara ta ɗauki lamarin da muhimmancin gaske, kuma za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen hukunta duk wani mai hannu a cikin lamarin. Za a tabbatar da adalci ba tare da saɓanin haka ba.

“Muna masu bayanin cewa, ‘yan bangan da suka aikata wannan ɗanyen aikin ba su da alaƙa da Dakarun Kare Al’umma na Jihar Zamfara.

“An ƙirƙiro Dakarun Kare Al’umma ne domin bai wa jama’ar jihar kariya amma ba kashe su ba.

“Muna sa ran wannan ƙarin hasken ya kawo ƙarshen ruɗanin da ke tattare da ko su wane ne waɗanda aka tsare game da kisan. Ba za mu taɓa saɓawa ba wajen kare rayukan al’ummarmu da dukiyarsu.

“Muna sanar da jama’a cewa Dakarun Kare Al’umma na Jihar Zamfara na da tsarin aiki wanda ba su gudanar da ayyukansu sai da jagororin hukumomin tsaro.

“Binciken farko da ‘yan sanda suka gudanar ya gano ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su tsohon ɗalibin malamin da aka kashen ne. Wannan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen fahimtar lamarin da kuma ɗaukar natakin da y dace.

“Gwamnatin Zamfara za ta bayyana wa jama’a sakamakon binciken da zarar ‘yan sandan sun kammala bincikensu.

“Kafin nan, muna jajanta wa iyalai da ‘yan uwan Sheikh Abubakar Hassan Mada da ma ɗaukacin al’umma. Da fatan Allah Ya jiƙansa,” in ji sanrwar.