Da yawan matan da suka yi kwantai dogon buri ne sila – Fatima Danborno

Hana lefe kawai ba zai iya samar da yawaitar yin aure tsakanin matasa ba – Saliha Zariya

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

Idan mai karatu bai manta ba, mun faro tattaunawa kan muhimmancin lefe a Ƙasar Hausa, inda muke tattaunawa da Hajiya Saliha Abubakar Abdullahi Zariya da kuma Fatima Ibrahim Garba Danborno.

A wannan satin za mu ɗora ne daga inda muka tsaya:

MANHAJA: Wasu na ganin yin lefe kan taimaka wa miji bayan aure, domin ya ɗauke nauyin sutura na tsayin lokaci. Sis Fatima, me za ki iya cewa kan hakan?

Yin lefe yana taimaka wa miji bayan aure sosai kuwa. Kamar ke ce ki siya sabbin kaya har kala goma ki ajiye. Ina ganin za ki rage fargaban me zan saka idan zanje bikin wane, ko kuma Sallah ta zo.

Su kansu mazan sun sani lefe yana taimaka masu sosai, shiyasa suke ƙoƙari wurin ganin sun yi lefen.

Rayuwar aure rayuwa ce da take yiwuwa ko babu lefe, muddin akwai ci da sha da kwanciyar hankali lefen nan ba komai ba ne. Sai dai kamar yadda na faxa a baya, mace tana son sabon abu, haka shi ma namiji yana son yaga matarsa tana shiga tana fita. Da yawan mata idan aka kawo lefensu, a cikin al’adar nan dai tana ɗiban tsofaffin ta kyautar da su. Tana yin hakan ne bayan taga ankawo mata lefe, idan ta ga me aka kawo mata sai tasan irin yadda kyautar take kasancewa. Dan haka kayan lefe ba namiji kaɗai yake taimakawa ba, har ita amaryar yana taimakonta.

Shi ya sa mu ba mu ce kada a yi lefe ba, amma ayi haƙuri da irin kayan da aka saka a ciki. Kowane ango yana burin yaga ya yi kayan kece reni a cikin akwatunan aurensa. Sai dai idan babu ba zai je ya yi sata ba, dole iya abin da yake da shi zai kawo. Ke kuma mace duk arhan kayan muddin ki ka iya amfani da su, za su yi maki kyau.

Akwai matar da na sani, ba mai kuɗi ta aura ba, kuma lefen da akayi mata babu armashi. Amma ko a jikinta. Atamfa mai arha takai akayi mata irin ɗinkin nan mai kyau da ɗaukar hankali. Wallahi sai shigarta ta fi kyau akan waɗanda suka saka mai tsadar.

Akwai lokacin da man shafawa zai ƙare. Amaimakon ta gaya masa ya siyo sai ta buɗe akwati ta ɗauko. Ko sabulun wanka da sauransu.

Don haka mafi rinjaye lefe ya fi taimakon maza, amma mu ma matan yana taimaka mana. Domin kafin rai ya ɓaci kafin a kawo mana abu, mun buɗe mun ɗauka.

Har wa yau dai muna kanki Sis Fatima, idan aka ba ki dama, ki samarwa lefe wurin zama na dindindim a aure, ko ki fitar da shi daga tsarin al’adun yin aure, wane za ki tabbatar, kuma meye dalili?

Tabdijan! Idan aka bani zaɓi akan yin lefe ko barinsa, zan iya cewa ayi lefen. Idan har akwai hali gwara a dinga yin lefe. Dalilaina anan kuwa su ne yin lefe yana taka rawa wajen samun sauyi tun daga yadda zata gudanar da rayuwarta a gidan aure har izuwa yadda zata dinga ji a zuciyarta ita amarya ce. Idan kuma har akace a soke lefe kamar yadda naga wani barista ya fito da bayanin an taɓa dakatar da yin lefe a Kano. Sai mu ce Alhamdulillah.

A bar wa iyaye siyawa yarinya kayayyakin da baza a rasa ba. Su kuma mazajen su dage su koma yi masu kayan ɗaki. Domin a wannan lokacin na matsi da muke ciki, iyayen yarinya sun fi shan wahala fiye da maganar haɗa lefe. Idan kuma ana ganin wannan al’adar tana da tasiri to a nawa ra’ayin gaskiya idan za ayi lefen kada a ce dole sai anyi ƙarya a cikinsa ba. Idan namijin zai yi kayan ɗakin kada a ce sai shima ya yi qarya a ciki. Duk da iyaye suna gudun maza su yi kayan ɗakin ne saboda gori. Eh tabbas gori yana taka rawa a wurin wasu matan da mazajensu ne suka yi masu kayan ɗaki.

Hajiya Saliha, lefe da kuma kayan ɗaki al’adu ne biyu da ake ganin idan an yi su an yi kunnen doki tsakanin vangaren amarya da kuma na ango. Shin kina ganin janye ɗaya ba tare da ɗaya ba zai iya samar da sauƙin da ake ganin za a samu a yin aure?

Ah ah. A nawa ra’ayin janye ɗaya a bar ɗaya ba zai wani samar da sauqin samu aure ba. Maimakon hakan zai fi kyau a gyara lamurran duka biyun domin kowannansu na da irin nashi fa’idan.

Abinda nike ganin ya dace akwai buƙatar malaman addini su shigo domin fadakarwa da gyaran waɗannan ababe guda biyu da yadda aka mayar da su tamkar ginshikin aure. Sai hukumomi su ma su saka dokar da ta dace wajen saita tunanin al’umma a rage riya da almubazzaranci yayin gudanar da harkar neman aure ko buki bakiɗaya.

Ba na tunanin hana lefe kawai zai iya samar da yawaitar yin aure tsakanin matasa domin ai ba lefen kaɗai ake riyar ba a wasu wuraren. Ina batun kayan na gani Ina so? Wanda za ki ga an kai katan-katan na minti, biskit, cingum da su huhun goro tamkar mutum zai buɗe shago?

Akwai masu kai katan hamsin, wasu ishirin ko goma, bayan katan-katan na ruwan sha da na lemu. Wannan fa tun kafin a kai ga batun kawo lefen ne za a yi, to kenan idan lefen kaɗai aka hana ai tsugunne bata ware wa samarin ba har dai talaka.

Sis Fatima kina da abin faɗa kan hakan?

Akwai tattaunawar da na yi da wasu mazan a cikin wani ‘group’, tabbas mafi rinjaye suna cewa idan aka soke maganar lefe za su iya yin aure. Wato muna cikin wani zamani ne Hajiya Saliha da da yawan maza suna tsoron wannan lefen. Idan ki ka duba a lokacin da barrister Abba Hikima ya ɗauko zancen soke lefe, ‘social media’ ta ɗauka da eh gaskiya a soke yin lefe, kuma da yawan masu maganar nan maza ne.

Hakan ya sa aka gane maza da yawa lefen nan yana firgita su. Da na tsananta binciken me ya sa lefe zai firgita maza har haka? Sai na gane daga gidan iyayen mata ne ake da wata ɗabi’a ta dogon buri. Sun ɗauki burin duniyar nan sun ɗora akan lefe.

Da ace iyaye za su gane, da su kansu ‘yan matan, su rage wannan dogon burin ina ganin da abun zai fi daidai. Matashi ne zai zo yana ‘yar sana’arsa ko yana da shagon ‘Provision.’ Kowa yasan shagon ‘provision’ babu ribar zo a gani.

Tayaya ki ke tsammanin idan an kawo zancen lefe na kece raini ba zai firgita ba? Ya san da zarar ya ce zai yi irin lefen da ‘yan mata suke da buri wannan shagon sai ya zama ana iya ƙirga kayan shagonsa.

Sis Fatima, sau dayawa za ki ga mata suna matsa lamba ga mazajen da za su aura kan sha’anin lefe, inda suke ganin sai irin lefen da ya dace da su za a yi masu, ko irin wanda aka yi wa wasu daga ƙawayensu, ba tare da la’akari da ƙarfin aljihu ba. Wane kira za ki yi ga irin waɗannan matan?

Kirana ga waɗannan matan su duba su ga yanayin da ake ciki. Ko daga gidan iyaye yanzu ya kamata kowacce budurwa ta duba taga yanayin rayuwar.

Duk da mata da yawa suna ɗorawa kansu dogon buri. Duk macen da a yanzu take ganin bazata iya aure ba, sai an yi mata lefe na gani na kece raini ko kuma ta haƙura da auren, zan iya cewa a gefe guda akwai dubunta da suke ganin ko babu lefe ba za su iya shiga kuma su yi zamansu lafiya lau.

A wannan zamani da muke ciki, wato ‘social media’ ya taka muhimmiyar rawa akan lefe. Kamar yadda na faɗa ne a baya, muddin muka ce karyar ‘social media’ ƙannenmu za su dauko, su ce da su za su yi koyi, ina tabbatar maki mata da yawa ba za su auru ba. Da yawan matan da suka yi kwantai, ko in ce suka ƙi auruwa a wannan zamanin, ba komai ke dawainiya da su ba, da ya wuce dogon buri. 80% ɗinsu duk suna hango wata rayuwa ce, da ko akwaita a zahiri bata yi yawan da zata zagayo kansu ba.

Ina baiwa ‘yan baya shawara su daina yarda lefe yana ruɗarsu har suke ganin za su iya haƙura da auren idan ba a yi masu ba. Su duba nagartar mijin, sannan su yi addu’a su zaɓi mijin aure. Insha Allahu ba za su taɓe ba.

Ko akwai wani bambanci a zamantakewar gidan aure da ke tsakanin macen da aka yi wa lefe da wadda ba a yi wa ba? Gare ki Hajiya.

Macen da ba a yiwa kayan lefe ba na iya kasancewa cikin ƙarancin suturar kwalliya saɓanin wacce aka yiwa. A nan kuma shi ango bai da damar qorafi domin shi ɗin ne bai kyautata ya yi ba.

Wasu iyayen kan yi ƙoƙarin yiwa ‘ya’yansu suturar ko tana gidan miji musamman idan sun fahimci bai da ƙarfi duk da ba ana nufin haka za a dauwwama ba.

Idan muka dawo fannin rayuwar auren gabaɗaya kuwa, tunanina sanin ma’anar auren da ingancin tarbiyyar ma’auratan ne zai haifar da kyakkyawar zamantakewa.

Duk macen da ta san tayi auren ne don raya sunnar Manzon Tsira, ta kuma yi shi ne don neman lada ba na tunanin don miji bai samu halin yi mata lefe zai gurvata nagartacciyar zamantakewar da suka iya shimfiɗawa kansu ba.

Sis Fatima na dawo gare ki, a wannan yanayi da muke ciki na matsin rayuwa, ya ki ke ganin ya kamata a ce lefe ya kasance?

Alhamdulillah! A nawa ra’ayin, ko kuma in ce a yanayin rayuwa da muke gani na yau da kullum! A ganina idan har ka tabbatar ba ka da ƙarfin yin akwatunan aure da yawa, ka kwantar da hankalinka ka je ka sami wannan amaryar tun kafin ma ka kai lefen.

“Jamila ina so mu yi magana akan lefenki. Na bubbuga iya abin da na samu na lefenki babu yawa. Atamfofi biyar ne, lesika uku, shadda biyu. Sai ‘yan kayan shafan da babu yawa da takalmi daya jaka ɗaya. Za ki iya yin haƙuri da su?”

Kin ga anan wurin ya fita haƙƙinta. Idan Allah ya taimake shi shi ɗin take so ba kayan lefe ba, zata yi masa fatan alkhairi da fatan su zauna lafiya.

Idan kuma yana da arzikinsa daidai misali. Zai iya yi mata akwatuna shida ko huɗu. Ya saka mata adadin kayan da suka kai ashirin ma ko fin hakan.

Kinsan fa akwai waɗanda har hayan kayan lefe suke yi. A cika kayan ƙarya aje akai. In taƙaice maki ma, akwai wanda ni ganau ce ba jiyau ba, ya kawo saitin akwatuna goma sha biyu, da manyan jakunkuna cike da kayan shafa. Idan ki ka ga kayan nan sai kin buɗe baki. Kowa yana ta mamaki, saboda ana ganin ƙarfinsa bai kai ba. Sai aka bar abin a matsayin karin maganar nan da ake cewa, ‘Mai zuciya ake gayawa biki ba mai dukiya ba.’

Kinsan abin mamaki? An yi biki da sati biyu, masu kaya suka ce lokaci ya yi. Ganin zai tozarta ya tura yarinya ta gaida iyayensa. Kuma a cikin kayan ya hanata ɗinka komai, ya kawo mata wasu set ɗin kayan da zata yi amfani da su. Ana ta murna ana cewa yarinya ta dace.

Bayan tafiyarta ya saka aka kwashe lefen nan tas! Ƙarshe dai yarinya haka ta yi rayuwa babu akwati ko guda ɗaya. Ya ce mata varayi ne suka ɓalla ƙofa suka shiga suka kwashe, ta kwantar da hankalinta zai kawo mata mafiyinsa. Har yau babu maganar akwati ko guda.

A ganina yin lefe hali ne, babu wanda zai tirsasa dan ba ka da hali ya ce dole sai ka yi yadda suke so.

Masu yin karyar saitin akwatuna ashirin ba a hana su ba, sun ga za su iya ne, suna da arzikin ne, amma don girman Allah a daina sakawa a ‘social media’ ana tsorata samarin ƙannenmu, ana kuma ƙarawa ƙannenamu mata dogon buri. Wallahi rayuwar nan ta yi wuya. Ba a hanaka idan kana da halin yi ba, amma a dinga sirrinta abin.

A kwatuna biyu uku idan shi ne iya ƙarfinka, ka lallava ka gayawa yarinya kafin ma a kawo, sannan ka miƙa kaya. A ganina yadda ake cikin matsin rayuwar nan ba sai an tsaya yiwa kowa bayanin yadda ƙasar nan ke ciki.

Kin tabo inda nake so in yi naki tambaya ta gaba, wato yayaɗa lefe bayan kawo shi. Shin kina ganin idan aka daina shelanta lefe, a wani vangare aka haramta yi masa rakiya da tarbon shi, ko yawon zuwa kallo, za a iya samun sauki ga yadda ake raina lefe, da kuma matsin lamba da wasu maza ke sha kan irin kayan da za su kawo?

Ƙwarai kuwa. A ra’ayina dole sai iyaye sun gane nunawa duniya lefe daidai yake da kawo dalilin rusa farin cikin amarya, ko kuma ƙananun maganganu.

Idan iyaye maza suka kawo lefe, mahaifin yarinya ko ƙaninsa ya karɓi kaya ya kai wani ɗaki a rufe. Ko dangin amaryar ba dole ba ne sai sun gani. Idan har aka koyi suturta lefe insha Allahu za a rage kaso mafi yawa daga cikin manyan dalilan da ke kawo rikici a dalilin lefe.

Ni a nawa nazarin ma, da ango zai ajiye wa amarya lefenta a gidanta, sai ya fi rufin asiri fiye da a ce wai an tafi ana shelantawa.