Sake fasalin hukumomin gwamnati: Tinubu ya bada umarnin ɗabbaƙa Rahoton Oronsanye

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin gaggawa jan ɗabbaƙa rahoton Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Sake Fasalin Hukumomin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Tarayya, Mr Stephen Osagiede Oronsaye.

Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris ya sanar da manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zatarwa (FEC) a Abuja a ranar Litinin.

Idris ya ce matakin zai shafi ma’aikatu da dama inda za a shafe wasu, sannan a gwamasu da wasu daidai da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Ya ce, “A yau Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki muhimmin mataki don amfanin ƙasa, inda ta bada umarnin aiwatar da Rahoton Oronsaye.

“Abin da wannan ke nufi shi ne, an shafe wasu ma’aikatu da hukumomi, an sake ma wasu fasali, yayin da an gwama wasu. Sannan an ɗauke wasu ma’aikatun zuwa wasu inda ake sa ran za su fi taɓukawa,” in ji Ministan.