Jarumar TikTok Murja Kunya, ta zargi Hisbah da cin zarafin matan da suka kama

Daga AISHA ASAS

Shahararriyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta zargi Hukumar Hisbah da cin zarafin mata da sunan gudanar da aikinsu.

Ta bayyana hakan ne a wani sautin murya da ta saki, wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta da dama.

Duk da cewa, zuwa yanzu babu wani tabbaci da zai iya tabbatar da lokacin da aka yi wannan sautin, wato an yi shi ne kafin ko bayan ta shiga komar hukumar, sai dai an tabbatar da sahihancin sautin da kuma zamewar sautin muryar jarumar.

A cikin sautin muryar, Murja ta yi bayyanin irin rawar da ita da abokanenta suka taka a yaƙin neman zaɓen gwamnan da ke kai yanzu na Jihar Kano, wato Abba Yusuf, a jam’iyyar sa ta NNPC.

A ranar Talata da ta gabata ne Hukumar Hisbah ta kama jaruma Murja Ibrahim Kunya, bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga maqwabtanta kan tuhumar ta da aikata ayyukan baɗala, waɗanda ke gurɓata tarbiyyar al’umma yankin, tare da hura wutar tashin hankula.

Akan haka ne, hukumar ta Hisbah ta kama Murja Kunya, tare da miqa ta ga kotun shari’a da ke zamanta a Kwana Hudu, inda kotun ta bayar da umurnin kai jarumar gidan gyaran hali da ke Kurmawa.

Sai dai ba da jimawa ba, aka samu labarin jarumar ta yi ɓatan dabo daga gidan gyaran halin, duk da cewa an tabbatar da zuwanta wurin ta sanadiyyar hotunanta a kwance a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan gyaran hali da suka karaɗe kafafen sada zumunta.

Lamarin fitar jarumar daga gidan yarin ya zama babban batun tattaunawa a kafafen sada zumunta a satin da ya wuce, duba da cewa, babu wani rahoton da ya sanar da kotu ta aminta da bada belin ta, ko hukumar ta Hisbah ta yi mata afuwa. Asalima sai da samun tabbacin fitar ta ne, sannan masu ruwa da tsaki kan lamarin suka magantu, ciki kuwa har da gwamnan jihar, wanda ya tabbatar da babu hannunsu a sakin Murja Kunya.

A wani ɓangaren kuwa mai magana da yawun hukumar gidan gyaran hali, Musbahu Ƙofar Nassarawa, ya ce, sun sake ta ne a bisa bin umurnin kotu.

Ita kuwa jarumar a cikin sautin muryar da ta saki, ta ce, “Allah (S.W.A) ya ji kukan mu da na iyayenmu da ‘yan uwa, ta hanyar amincewa da miqa mulki ga wannan gwamnati da ke ci a yanzu, sai dai Daurawa da ahalinsa na iya ƙoƙari wurin shafawa wannan gwamnati kashin kaji da sunan Hisbah.

Sun je otal ɗin Sarina, sun kama ‘yan mata, sun zuba su a motocinsu kamar biredi, sannan su kai su gidan kaso.

Wallahi na rantse, ba ƙarya nake masu ba, idan dakarun Hisbah suka kama mace a otal, suna cin zarafin ta fuskar jima’i.

Su kan ba wa matan zaɓi na ko dai su amince da yin lalata da su, irin istimna’i ko wasa da nonuwan matan, ko kuma su kai su ga iyayensu.”