Gasiyar abin da ya faru ga jaruma Maryam CTV

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A ‘yan kwanakinnan babu wani labari da ya karaɗe dandalin sada zumunta kamar na haɗarin da jarumar Kannywood Maryam Sulaiman wadda aka fi sani da Maryam CTV ta yi, wadda ta haɗu da haɗarin ne a ranar Asabar da ta gabata 10 ga Fabarairu, 2024.

Labarin ya ɗauki hankalin mutane sosai saboda irin yadda aka rinƙa bayar da labarai masu karo da juna da kuma ƙarin gishiri a game da abinda ya faru.

Wasu sun rinƙa bada labarin cewa, jarumar ta samu mummanan haɗari ta karairaye a hannu da ƙafa. Wasu kuma suke bada labarin ƙafafun ta ne suka yi rugu-rugu da hannayen ta don haka ba ta san ma halin da take ciki ba, da dai sauran labarai irin na ƙanzon kurege kala-kala.

Domin jin yadda gaskiyar haxarin da Maryam CTV ta yi da kuma sanin halin da take ciki a yanzu, wakilinmu ya samu Maryam CTV a gidanta da ke Unguwar Hotoro a cikin garin Kano in da ya same ta a zaune a kan kujera a falonta tare da masu zuwa duba ta.

Mun tambaye ta ko me ya faru da ita kuma a wanne hali take ciki a yanzu?

Maryam CTV: To gaskiya abin da ya faru da ni shi ne, a ranar Asabar ɗin da ta gabata da misalin ƙarfe ɗaya na rana na fita unguwa a kan adaidaita sahu ‘Keke Napep’ to ka san dai kowanne mutum a duniya da irin ƙaddarar sa, kuma in dai mutum yana raye zai riski ƙaddarar sa, to kuma alhamdulillahi ƙaddara ta sauka a kaina amma kuma ta zo da sauƙi ba kamar yadda mutane suke ta yaɗawa ba.

Ƙaddara ce ta tsautsayi na hau ɗan adaidaita sahu zan je Zoo Road a daidai kwanar Sabo da ke Hotoro wani mai moto ya zo ya daki bayan adaidaita sahun da muke ciki ni da ƙawata, to shi kuma adaidaita sahun da muke ciki sai ya daki wata mota sai ya faɗi da mu ya juya, wanda sakamakon wannan abin sai ƙarfen adaidaita sahun ya danne mini hannu shi ne na samu karaya a hunnuna na hagu waje biyu, wanda a yanzu halin da na samu kaina a ciki kenan.

Amma ana ta yaɗa labarin cewar kin samu karaya hannu da ƙafa duk kin karairaye ba ki san ma a inda ki ke ba.

To gaskiya ba haka ba ne, don kaima a yanzu kana tare da ni a yanzu muna magana ba kamar yadda ake faɗa na karkarye hannu da ƙafa ba don ƙafa ta babu karayar komai sai dai ɗan kujewa irin na faɗuwa da kuma hannuna na dama. Amma wannan karayar ta hannun hagu ita ce dai ciwon ta na samu ban kakkarye rugu-rugu ba, saboda ana ta bugo mini waya daga garuruwa da dama har ma daga Nijar da sauran wasu ƙasashe ana tambayar cewa na samu ciwo na karairaye na fita hayyacina ban san kowa a kaina ba wallahil azim ƙarya ne, ko lokacin da abin ya same ni a cikin hayyacina nake na san abin da nake yi har muka je asibiti aka yi mini aiki sannan aka kaini wajen ɗorin gargajiya aka yi mini babu abin da na manta, babu kuma abin da ban sani ba.

A yanzu ina gidana kamar yadda ka zo ka same ni, saboda ka ga ɗorin gida aka yi mini, kuma sakamakon ba mai tsanani ba ne sosai ka ga wajen da na karye ɗin tsakiyar hannu ne tsakanin gwiwar hannu zuwa gaɓa duk kusan a waje ɗaya ne karayar suna kusa da kusa don ɗayan ma sai da ƙashin ya bulluƙo sai da aka mayar da qashin aka yi ɗinki sannan aka zo aka yi ɗorin kuma ina sa ran nan gaba kaɗan za a samu sauƙi da yardar Allah don ka ga ko zama ban yi ba a asibitin sun duba ni ne suka yi mini aikin da za su yi suka ba ni magunguna da allurai kuma sai aka yanke shawarar a je a yi ɗori na gargajiya.

Don haka na je Kofar Na’isa gidan Sarkin maɗora a nan ‘ya’yansa suka yi mini ɗorin, kuma a cikin ‘ya’yan sa ma akwai likita don shi ne ma ya mayar mini da wannan ƙashin da ya bulluko ya gyara sannan ya ɗinke sai suka zo suka yi ɗorin daga baya.


Don haka saƙona ga masoyana, don Allah ku kwantar da hankalinku, na san irin wannan abin da tashin hankali, duk wanda ka ke so ba ka son wata masifa ko bala’i ya same shi, to don Allah a yi haƙuri abu ne na ƙaddara kuma ya faru kuma da yarda Allah za a samu sauƙi.

Don haka ina godiya ga dukkan waɗanda suka damu da halin da nake ciki suke ta bugo wayoyi da saƙon kar ta kwana, da na WhatsApp daga ƙasashe da dama daga gari gari. Kuma godiya ga masu zuwa gida suna duba ni wanda tun daga ranar da abin ya faru har zuwa yanzu kullum jama’a zuwa suke yi daga safe har zuwa dare. Na gode Allah ya saka da alheri.