‘Yar Nijeriya ta lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta ƙasa da ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Wata matashiya mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi daga Jihar Gombe ta lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta Mata zalla ta Ƙasa da Ƙasa da aka gudanar a ƙasar Jordan.

Hajara Ibrahim wadda ɗalibar makarantar Islamiyyar Abubakar Siddiq ce kuma ‘yar aji biyu a Jami’ar Jihar Gombe, ta zo ta ɗaya ne a rukunin masu karanta izifi 60 da Tajwid a tsakanin ƙasashe 39 da suka fafata a gasar.

Wannan shi ne karo na 18 da ake shirya wannan gagarumar gasar karatun Ƙur’ani ta mata zalla a ƙasar ta Jordan.

Yayin gasar wadda ta gudana daga 17 zuwa 22 ga Fabrairun 2024, Hajara ta samu maki 99.5 wanda hakan ya ba ta damar zama gwarzuwar gasar.

Tuni dai Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya, ya miƙa saƙon taya murna ga Hajara da iyalanta da malamanta bisa samun wannan nasarar, tare da yaba ƙwazonta dangane da karatun Alƙur’ani.

Gwamna ya kuma yi amfani da wannan dama wajen nuna wa al’umma muhimmancin bai wa matasa ilimi.

Ana sa ran Gwamna Inuwa ya karɓi baƙuncin Hajara a ofishinsa bayan ta dawo gida daga wajen gasar.