Babban Labari

Tinubu ya ɗauki tsauraran matakai kan tsaro da yunwa

Tinubu ya ɗauki tsauraran matakai kan tsaro da yunwa

*Gwamnoni za su yi ’yan sandansu*Ya umarci shugabannin tsaro su dirar wa masu ɓoye abinci Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnoni suka amince da kafa ’yan sandan jihohi a ƙasar. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ƙarshen wani taron gaggawa da shugaban ya kira a zauren majalisar da ke Fadar Shugaban Qasa a Abuja. Ministan ya ce, za a gudanar da tarurruka da dama,…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Hukumar Kula da Fetur na shirin ɗauke muhimman sassanta zuwa Legas

Da Ɗumi-ɗumi: Hukumar Kula da Fetur na shirin ɗauke muhimman sassanta zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Man Fetur ta Ƙasa da aka fi sani da Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission a Turance, na duba yiwuwar ɗauke wasu muhimman sassanta zuwa Legas, kamar yadda wata takardar bayani wadda News Point Nigeria ta samu leƙawa ta nuna. Takardar mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2024 ta ce, an yanke shawarar haka ne domin bunƙasa ayyukan hukumar, rage yawan kuɗin da hukumar ke kashewa wajen gudanar da ayyukanta da kuma tabbatar da hukumar na morar kadarorinta a Legas. A cewar takardar, “Bisa manufar bunƙasa ayyukan hukumar da cigaban masana'anta da kuma…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya bai wa ’yan wasan Super Eagles tukwicin filaye da gidaje bayan dawowa daga Gasar AFCON 2023

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya bai wa ’yan wasan Super Eagles tukwicin filaye da gidaje bayan dawowa daga Gasar AFCON 2023

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya karrama ‘yan wasan Super Eagles da lambar yabo ta MON hadi da tukwicin fili da gida a birnin tarayya Abuja. Tinubu ya yi wa ‘yan wasan goma ta arzikin ne a ranar Talata a lokacin da ya karbi bakuncinsu tare da jami’an Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Tawagar ta ziyarci Tinubu ne bisa jagorancin Ministan Bunkasa  Wasannin Motsa Jiki, Saenata John Owan Enoh. Wata sanarwar da ya fitar, Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya ce Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar Super Eagles bisa…
Read More
Yadda ake tunkarar tsadar rayuwa a Nijeriya

Yadda ake tunkarar tsadar rayuwa a Nijeriya

*Kotu ta tsoma baki*Bankin CBN ya yi bayani*Jiga-jigan gwamnati sun rufe ƙofa*Shin zanga-zanga mafita ce? Daga MAHDI M. MUHAMMAD Matsalar tsadar rayuwa ta zama babban abinda a yau a Nijeriya aka fi tattaunawa a kai, saboda yadda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabo a kullum, yayin da talakawan ƙasar ke faɗi-tashin ganin sun tsira daga yanayin sakamakon yadda ƙarancin abin hannu ke cigaba da ta’azzara. A ɗaya ɓangaren kuwa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta na iƙirarin cewa, lallai ta na yin iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta shawo kan lamarin, wanda masana da masu nazari da dama…
Read More
Kotu ta umarci Gwamnatin Nijeriya ta daidaita farashin fetur, madara, sukari keke da sauransu

Kotu ta umarci Gwamnatin Nijeriya ta daidaita farashin fetur, madara, sukari keke da sauransu

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Legas ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako daya a kan ta daidaita kayayyakin masuru a fadin kasa don amfanin ‘yan kasa. Kayayyakin da lamarin ya shafa sun hada da madara, sikari, gishiri, keken hauwa, babur, fetur, gas, kananzir da sauransu. Kotun ta ba da wannan umarni a zaman da ta yi a ranar Laraba karkashin jagorancin Mai Shari’a Ambose Lewis-Allagoa. Alkalin ya bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta daidaita farashin kayayyakin ne biyo bayan karar da Babban Lauyan Nijeriya kuam mai rajin kare hakkin dan’adam, Femi Falana SAN ya shigar Kotun.…
Read More
Binciken tsaro ya bankaɗo shirin neman gwara kan Sanatocin Arewa da na ’yan ƙasa

Binciken tsaro ya bankaɗo shirin neman gwara kan Sanatocin Arewa da na ’yan ƙasa

Daga BASHIR ISAH Wasu jami’an hukumomin tattara bayana asirri na kasa sun bankado shirin da wasu makirai ke yi na neman gwara kan sanatocin Arewa a Majalisar Tarayya  da talakawansu. Jami’an wadanda suka bukaci a sakaya sunansu su shaida wa jaridar PRNigeria cewa har wa yau, shirin na da nufin gwara kan hukumomin tsaron kasar nan don su rika ganin laifin juna game da matsalar tsaron kasa. Sun bayyana hakan ne a matsayin martani a kan wani rahoto wanda ya yi zargin hukumomin tsaron sun kafa idanunsu kan wani Sanatan Arewa saboda zarginsa da ake yi da daukar nauyin ta’addanci,…
Read More
Ya yi wuri a yanke ƙauna da Tinubu – Idris

Ya yi wuri a yanke ƙauna da Tinubu – Idris

*Shugaban yana aiki dare da rana don gyara Nijeriya, inji ministan labarai Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya roki ‘yan Nijeriya da su kara hakuri da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa, ya yi wuri a yanke kauna ko a dawo daga raikiyar gwamnatin daga lokacin da ya dare gadon mulki zuwa yanzu. Tun da ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, Shugaba Tinubu ya bullo da wasu tsauraran sauye-sauye a fannin tattalin arziki, irin su shakewar Naira da kuma cire tallafin man fetur…
Read More
EFCC ta bankaɗo ƙungiyar addini tana samo kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci

EFCC ta bankaɗo ƙungiyar addini tana samo kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta bankado yadda wata kungiyar addini a Nijeriya ke tafka almudahana don daukar nauyin ta'addanci. Kazalika ya bayyana yadda suka sake gano wata kungiyar addini da ke ba da kariya ga wani mai karkatar da kudade bayan gano wasu kudade a asusun kungiyar da ake zargin na sata ne. Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a ranar Larabar a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja, yayin wata tattaunawa ta yini daya kan “Matasa, Addini da Yaki da Rashawa.” A cewar Olukoyede, EFCC ta yi…
Read More
Maida hukumomin gwamnatin Legas: Soki-burutsu ’yan siyasar Arewa ke yi, inji Sanusi

Maida hukumomin gwamnatin Legas: Soki-burutsu ’yan siyasar Arewa ke yi, inji Sanusi

*'Yan Nijeriya na cece-kuce kan dauke canja mazaunin CBN da FAAN Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M MUHAMMAD Mai Martaba Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce, “surutu” da soki-burutsu kawai ’yan siyasar Arewa ke yi dangane da shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na dauke ragamar gudanarwa na wasu sassan bankin daga Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja zuwa birnin Legas, wanda shi ne tsohon hedikwatar kasar. Sarki Sanusi ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa da su yi watsi da surutan da ‘yan siyasar Arewa ke yi kan batun, saboda a cewarsa, Abuja a matsayin Babban…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara biyar kan Farouk Lawan

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara biyar kan Farouk Lawan

Daga BASHIR ISAH Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekara biyar da a baya kotu yanke kan a kan tsohon dan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan, bayan da ta kama shi da laifin karbar cin hancin $500,000 daga hannun Femi Otedola. Lawan ya daukaka kara zuwa Kotun Koli ne inda ya nemi kotun ta yi watsi da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a kansa ran 24 ga Fabrairun 2022 wanda ta daure shi shekara biyar a gidan yari. Sai dai, hukuncin da Mai Shari’a John Okoro ya rubuta wanda Mai Shari’a Tijjani Abubakar karanta, kotun ta yanke cewa…
Read More