Babban Labari

Ɗauke ragamar sassan CBN zuwa Legas: Cika baki kawai kuke, cewar Sanusi ga ’yan siyasar Arewa

Ɗauke ragamar sassan CBN zuwa Legas: Cika baki kawai kuke, cewar Sanusi ga ’yan siyasar Arewa

Daga BASHIR ISAH Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi, ya ce “surutu” kawai ‘yan siyasar Arewa ke yi dangane da shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na dauke ragamar gudanarwa na wasu sassan bankin daga Abuja zuwa Jihar Legas. Sanusi ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa da su yi watsi da surutan da ‘yan siyasar Arewa ke yi kan batun saboda a cewarsa, Abuja a matsayin Babban Birnin Tarayya ba matsalar Arewa ba ne. Idan dai za a iya tunawa, tun bayan da CBN ya bada sanarwar shirinsa na dauke wasu muhimman sassan CBN daga Abuja zuwa Legas, aka yi…
Read More
Ndume ya gargaɗi Tinubu kan shirin ɗauke CBN da FAAN zuwa Legas

Ndume ya gargaɗi Tinubu kan shirin ɗauke CBN da FAAN zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar Datawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya gargadi Shugaban Kasa Bola Tinubu game da shirin da yake da shi na mayar da ragamar wasu muhimman bangarorin CBN da kuma Hedikwatar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) zuwa Jihar Legas. Ndume ya ce muddin hakan ta tabbata, akwai sakamakon da zai biyo baya a siyasance. Ya ce, “Ba za mu yarda da wannan ba. Hasali ma, ba taimakon Shugaban Kasa suke yi ba, domin kuwa hakan na da sakamako a siyasance” Sanatan ya yi wadannan kalaman ne yayin wata tattauna da…
Read More
Matsalar tsaro: Majalisar Dattawa za ta sammaci Ministan Abuja

Matsalar tsaro: Majalisar Dattawa za ta sammaci Ministan Abuja

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta ce ta kimtsa domin gayyato Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zo ya yi bayani game da tabarbarewar tsaro a Birnin Tarayya. Sanata mai wakiltar Birnin Tarayya a Majalisar, Ireti Kingibe ce ta bayyana haka yayin wata tattaunawa da tashar Channels TV ta yi da ita a ranar Lahadi. Ta ce idan majalisar ta dawo bakin aiki, za a gayyato Wike a matsayinsa na Ministan Abuja don ya zo ya yi bayanin matakan da yake dauka domin dakile matsalar taro a birnin na tarayya. A cewar Sanatar, “Ina da yakinin za a gayyace shi. Amma…
Read More
Fargabar tsaro ta dawo a hanyar Abuja

Fargabar tsaro ta dawo a hanyar Abuja

*Mutane sun fara hijira a yankin Bwari*’Yan bindiga sun kashe magidanci, sun sace ’ya’yansa 13*An ceto wanda aka sace daga Abuja zuwa Kano Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu al’umma sun sake fadawa cikin fargabar rashin tsaro a yankin kewaye da hanyar Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja biyo bayan yadda a kwana-kwanan nan masu garkuwa da mutane ke yi wa mutane dauki dai-dai. Rahotanni sun nuna cewa, wasu magidanta mutane sun fara yin hijira daga yankin Bwari, wanda ke kan iyakar Abuja ta vangaren Jihar Kaduna tun bayan shigowar sabuwar shekarar nan ta 2024, bayan kashe wani magidanci da…
Read More
Hukuncin Kotun Ƙoli, siyasa da tsaro a Kano

Hukuncin Kotun Ƙoli, siyasa da tsaro a Kano

*Yadda gwamnonin wasu jihohi ma ke fuskantar makomarsu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A safiyar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024, Kotun Kolin Tarayyar Nijeriya ta yanke hukunci mafi sarkakiya, tsumayi da zulumi a babban zaben kasar na 2023, wato shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin kasar. Bugu da kari, a Juma'ar ce kuma Kotun Kolin ta yanke hukunci kan zaben kujerun gwamnan jihohin da suka hada da Legas, Zamfara, Filato, Ebonyi, Bauchi da Kuros Ribas, kamar yadda alkalan kotun suka sanar. A karshen watan Disamba ne dai Kotun Kolin ta jingine hukunci akan karar da Gwamnan Jihar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafi ƙarƙashin NSIPA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafi ƙarƙashin NSIPA

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafin da ke karkashin kulawar Hukumar Shirin ba da Tallafi ta Kasa (NSIPA). A cewar Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Taryya, Segun Imohiosen, an dauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da bincike yadda ya kamata kan zargin almundahana a hukumar. Sanarwar ta ce, Fadar Shugababn Kasa ta bayyana cewa, an dakatar da baki daya shirye-shiryen bayar da tallafi guda hudun da ke karkashin NSIPA, na tsawon makonni shida. Shiryen-shiryen da lamarin ya shafa sun hada da Shirin N-Power, Shirin Conditional Cash Transfer, Shirin…
Read More
Abba Yusuf ya kai bantensa a Kotun Ƙoli

Abba Yusuf ya kai bantensa a Kotun Ƙoli

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kotun Koli ta battabar da nasarar da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu a zaben 2023 a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano. A ranar Juma’a Kotun Kolin ta kawo karshen gardamar da ake yi tsakanin Abba Kabir da Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC dangane da shugabancin Jihar Kano. Yayin yanke hukuncin, alkalan kotun sun tabbatar da cewa, Kotun Daukaka Karar ta yi rashin fahimta na soke kuri’u 165,616 na Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta yi. Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya kuma bayyana cewa batun kasancewar Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano

Kotun Ƙoli ta ayyana Juma'a ta wannan makon a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano da ke gabanta. Sakataren tawagar lauyoyin Jam'iyyar NNPP, Barista Bashir Tudun Wazirci, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai. “Gaskiya ne, an tabbatar da hakan a hukumance. Sun faɗa mana mu zo kotu ranar Juma'a don yanke hukunci. "Sun shaida mana kada kowane ɓangare ya zo da lauyoyin da suka wuce biyu," in ji Barista Bashir.
Read More
Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarni kan a dakatar da Ministar Jinkai da Yaki da Talauci, Dokta Betta Edu daga mukaminta na minista. Kuma dakatarwar ta fara aiki ne nan take, kamar yadda Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya sanar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Betta ne domin kare mutuncin gwamnatin kasa da kuma aiki da gaskiya. Ta kara da cewa, Tinubu ya bai wa Shugaban EFCC umarni kan gudanar da cikakken bincike a kan Betta bisa zargin da ake yi mata na karkatar da wasu makudan…
Read More