07
Jan
*Badaqalar ta shafi jami’o’i 78 *An cafke jami’ai bisa zargin hannunsu *Hukumar NYSC ta farga Daga MAHDI M. MUHAMMAD A farkon makon nan ne Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da amincewa da takardar shaidar digiri daga wasu jami’o’in kasashen waje da ma masu cibiya a cikin gida. Umarnin na qunshe ne a cikin wata sanarwa ne da aka fitar a ranar Talata, 2 ga Janairu, 2023, mai dauke da sa hannun Augustina Obilor-Duru a madadin Daraktan Yada Labarai Da Hulda Da Jama’a Na Ma’aikatar Ilimi Ta Tarayya. Gwamnati ta koka da cewa "wasu 'yan Nijeriya suna amfani da hanyoyin da…
