Tsadar Rayuwa: ‘Abin da muka shuka muke girba’ – Shettima

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Matamakin shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa abin da aka shuka a baya shi ake girba a yanzu dangane da tsadar rayuwar da ake fuskanta a ƙasa.

Shettima ya buƙaci ‘yan Nijeriya da a kula da yadda suke bayyana fushinsu game da matsalolin tattalin arzikin da ƙasa ke fama da su a wannan hali.

Ya ce dukkanin abubuwan da ake gani a yanzu sakamakon abubuwan da aka aikata a gwamnatocin a baya ne wanda ƙasar ke ƙoƙarin daidaita komai don inganta tattalin arzikin ƙasa.

Ya ci gaba da cewa, kamar kowace gwamnati, ita gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta zo da nata tsare-tsare da nufin inganta tattalin arziƙin ƙasa, yana mai cewa gwamnati mai ci ba ta da wata manufa ta gana wa ‘yan ƙasa uƙuba.

Shettima ya yi wɗannan kalaman ne a wajen taron lacca wanda ƙungiyar tsoffin ɗalibai Musuli ta Jami’ar Legas Musulmi da ta shirya a ranar Lahadi.

Ya yi jawabin ne ta bakin wakilinsa a wajen taron, Dokta Hakeem Baba-Ahmed wanda ya kasance mai ba shi shawar kan harkokin siyasa.

Shettima ya kara da cewa, duk da ƙalubalan da hakan ke haifar wa ‘yan ƙasa, gwamnatin Tinubu na yin abin da take yi ne domin daidaita ƙasar kan turbar da ta dace domin samun gobe mai armashi.

A ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi fatan Allah Ya kai mu Ramadan, Ya kuma ba mu ikon aiwatar da ibadar da Ya ɗora mana.

‘Yan Nijeriya na kokawa da tsada da ƙuncin rayuwar da suke fuskanta wanda wasu ke ra’ayin hakan ya samo taushe ne tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur a watan Mayun bara.

By Editor