Daga BASHIR ISAH
Hukumomi a yankin Ƙaramar Hukuma Kano Municipal sun tabbatar da ɓullar cutar ƙyanda a wasu sassan yankin.
Kodinetan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na yankin, Alhaji Aliyu Jinjiri Kiru, shi ne ya bayyana haka yayin taro da kwamitin bada agajin gaggawa da suga shirya a sakatariyar hukumar a ranar Asabar da ta gabata.
Cikin sanarwar da ta fitar, Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Fatima Abdullahi, ta naƙalto Kodinetan ya ce, sun samu rahoto daga cibiyoyin kula da lafiya a sassan yankin game da ɓullar cutar ƙyada da sauran cututtuka.
Jami’in ya ƙara da cewa, wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da Sharada, Madatai, da kuma Gandun Albasa.
Daga nan ya yi kira da a gaggauta ɗaukar matakan davsuka dace domin daƙile yaɗuwar cutar.
A nasa ɓangaren, jami’i mai kula da yaƙi da yaɗuwar cututtuka na hukumar, Tukur Hassan, ya ce sun rigada sun tura waɗanda aka samu ɗauke da cutar zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala don killace su.
