Daga BASHIR ISAH
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta ƙaryata rahotannin da suka ce rumbun kayan abincin da ɓatagari suka wawashe ranar Lahadi a yankin Abuja mallakarta ne.
Mai magana da ywun NEMA, Manzo Ezekiel ne ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.
A ranar Lahadi wasu ɓatagari suka fasa rumbun kayan abinci mallakar Sashen Harkokin Noma na Hukumar FCT tare da wawashe kayayyakin da ke adane cikinsa.
Wani jami’in sashen, Zakari Aliyu, shi ne ya tabbatar wa tashar Channels Television hakan ta saƙon SMS da ya aike mata cewa rumbun mallakar sashen harkokin noman ne.
NEMA ta ƙara da cewa, faruwar hakan ya sa ta ƙara tsaurara matakai wajen kula da ma’adanata da ke sassan ƙasa.
“Domin ci gaba da kula da kayayyakin NEMA, Darakta-Janar Mustapha Habib Ahmed ya bai wa daraktocin hukumar na shiyyoyi da su ƙarfafa tsaro wahen kula da rumbunan hukumar da ke faɗin ƙasa,” in ji NEMA
