An dakatar da cire tallafin fetur a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ƙarshe dai, Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar tsawaita wa’adin cire tallafin man fetur har bayan wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari a karagar mulki.

Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wannan Alhamis yayin da ta ke zantawa da manema labarai a Abuja.

A cewarta, Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa NEC ce ta yanke shawarar cewa ba yanzu ne lokacin da ya dace a cire tallafin man fetur ba a ƙasar.

Ministar wadda ta bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ta ce dole ne a sake nazari tare da taka-tsantsan dangane da raɗaɗin da ’yan Nijeriya za su fuskanta sanadiyyar janye tallafin man.

Ta ce, a yanzu shirye-shiryen da tuni sun yi nisa za su ci gaba da gudana musamman ta fannin tuntuvar dukkanin masu ruwa da tsaki ciki har da wakilan sabuwar gwamnatin Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Zainab ta ce, “Majalisar ta amince da cewa dole ne a cire tallafi na farko cikin gaggawa ba tare da wani ɓata lokaci ba, domin kuwa ba abu ne mai ɗorewa ba.

“Ba za mu iya ci gaba da biya ba. Dole mu kalli yadda cire tallafin ba zai jefa rayuwar ’yan Nijeriya ba cikin mawuyacin hali.

“Akwai buƙatar neman mafita bayan cire tallafin muna buƙatar yin shiri game da hakan domin tabbatar da an taimaka wa mutane da cire tallafin zai shafa.”

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta karvo aron dalar Amurka miliyan 800 daga Bankin Duniya domin sassauta wa mutane raɗaɗin cire tallafin.