‘Yan sanda sun kashe gawurtattun ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda a Jihar Katsina sun ga bayan gawurtattun ‘yan bindiga, Shehu Tsauni da Duna a jihar.

Haka nan, ‘yan sanda sun ƙwato bindiga ƙirar AK 47 guda biyu daga hannun ‘yan fashin dajin.

Bayanai sun ce, ‘yan sanda sun halaka ɓarayin ne bayan da suka yi yinƙurin yin garkuwa da wani fitaccen ɗan kasuwa a jihar.

Majiyarmu ta ce lamarin ya auku ne a ranar Alhamis bayan da bayanan sirri suka riski sashen yaƙi da garkuwa da mutane na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar.

Ta ƙara da cewa, bayan musayar wutar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindigar, daga bisani aka gano gawarwakin Samaila Shehu Tsauni na ƙauyen Tsaunin Kura da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi da Duna Bakare.

An ce Shehu ƙasurgumin ɗan bindiga ne wanda aka tsare a 2020 dangane da harin da aka kai GSS Malumfashi tare da gurfanar da shi a kotu a wancan lokaci.

Yayin da shi kuwa Duna ya jagoranci kai hari sau da dama haɗi da garkuwa da mutane a Mabai da Batsari da kuma Kalgon Malam a baya-bayan nan.

Kakakin ‘yan sandan jihar, CSP Gambo Isah, ya faɗa a ranar Juma’a cewa, ana ci gaba da bincike, kuna za a fitar da cikakken rahoto bayan kammala binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *