04
Feb
Daga AISHA ASAS Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ta aminta da batun samar da sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda 20 a faɗin ƙasa. Majalisar ta cim ma wannan matsaya ne yayin zamanta na Larabar da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya ce, jami'o'in za su samu lasisin zarafin gudanarwa ne daga hannun Hukumar Kula da Jami'o'i ta Ƙasa (NUC), wanda za su yi amfani da shi nan da shekaru uku masu zuwa, yayin da gwamnati za ta ci gaba da sanya musu ido. Jami'o'in da Majalisar ta amince da a kafa ɗin…