Za mu ladabtar da Tinubu kan kalaman da ya zazzaga wa Buhari – Adamu

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC ta ce za ta ladabtar da jagoranta na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, saboda kalaman da ya zazzaga wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kwanan nan.

Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja a ranarAsabar da ta gabata.

Idan za a iya tunawa, a kwanan nan aka ga wani bidiyon Tinubu na yawo yayin ziyarar neman ƙuri’un daliget da ya kai Jihar Ogun, inda a ciki bidiyon aka ji shi yana kalamai kan taimakon da ya yi wa Buhari da wasu ‘yan siyasa wajen cin zaɓe a baya.

Sai dai, duk da Tinubu ya fitar da wata sanarwa a Juma’ar da ta gabata don ƙarin haske da kuma ba da haƙuri kan kalaman nasa, amma Sanata Adamu ya ce haƙurin da bayar ɗin bai wadatar ba, sai ya fuskanci ladabtarwa.

“Mai yiwuwa mu ladabtar da shi (Tinubu) dangane da kalaman da ya yi a kan Buhari,” inji Adamu.