Gwamnonin APC na Arewa sun amince Buhari ya zaɓi magajinsa a Kudu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnonin APC na jihohin Arewa da wasu masu faɗa a ji a jam’iyyar, sun buƙaci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya zaɓi wanda zai gaje shi daga cikin takwarorinsu na Kudu.

Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne yayin zaman da suka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Yayin zaman nasu, gwamnonin sun buƙaci ‘yan takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa a kan su janye su bai wa ‘yan Kudu wuri su fafata.

“Muna roƙon dukkan ‘yan takara daga jihohin Arewa a kan ku janye ƙudirin takararku don amfanin ƙasa, sannan ku bar ‘yan takara daga Kudu kaɗai su shiga zaɓen fidda gwani.

“Mun ji daɗi matuƙa da matakin da ɗan uwanmu, Mai Girma Gwamna Abubakar Badaru ya ɗauka na janye aniyar takararsa.

“Aiki ne a kan APC tabbatar da an samu sakamako mai kyau a zaɓuɓɓukan 2023 don ci gaba da gina ƙasa.

“Don haka muke kira ga ɗaukacin shugabannin APC kowa ya yi ƙoƙarin sauke nauyin da ya rataya a kansa,” inji gwamnonin.

Mahalarta taron sun haɗa da Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, Abubakar Sani Bello na Neja, Abdullahi A. Sule na Nasarawa, Farfesa B.G. Umara Zulum na Borno da kuma Nasir Ahmad El-Rufai na Kaduna.

Sauran su ne, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, Bello M. Matawalle na Zamfara, Simon Bako Lalong na Filato, tsohon Gwamnan Sakkwato, Aliyu Wamakko, Dr. A.U. Ganduje na Jihar Kano, sai kuma Sanata Abubakar Atiku Bagudu na Kebbi.