23
May
Daga BASHIR ISAH Jam’iyyar APC ta ɗage zaɓen fidda gwanin na ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da ta shirya gudanarwa a ranar Litinin, 23 ga Mayun 2022, tare da cewa za ta sanar da sabon lokaci nan gaba. Duk da dai jam’iyyar ba ta ba da dalilin ɗage zaɓen ba, amma ba wannan ne karon farko da APC ta sauya jadawalin zaɓen fidda gwanin nata ba dangane da shirye-shiryen zaɓen 2023. Sanarwar da ta nuna ɗage zaɓen ta ce, “An ɗage shirin tantace ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 23 ga Mayun 2022. “Za a sanar…
