31
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta naɗa mamallakin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City da ke Ingila, Sheikh Mansour bin Zayed a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Ƙasar. A cikin wata sanarwa da Kamfannin Dillancin Labaran ƙasar na Wam ya wallafa, ƙasar ta ce attajirin ya ɗare kujerar ce a matsainsa na shugaban gwamnati. Shugaban Ƙasar ne dai ya sanar da amicewar naɗin, inda ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Ƙolin Ƙasar na naza Sheikh Mansour a matsayin. Kafin naɗin nasa dai, attajirin shi ne Mataimakin Fira Ministan ƙasar. Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya ayyana sunan…
