Wasanni

An zaɓi Samuel Eto’o ya zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Kamaru

An zaɓi Samuel Eto’o ya zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Kamaru

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An zaɓi shahararren ɗan ƙwallon Kamaru, Samuel Eto’o a matsayin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (FECAFOOT) a ranar Asabar, wata ɗaya kafin ƙasar ta karɓi baƙuncin gasar cin kofin Afrika. Tsohon ɗan wasan gaba Eto’o, wanda ya taka leda a Barcelona, Inter Milan da Chelsea, zai karɓi ragamar ƙungiyar da ta daɗe tana fama da rigingimu, rashin gudanar da mulki da kuma zargin cin hanci da rashawa. Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta shiga tsakani sau da yawa don kawo ƙarshen cece-kuce tsakanin jami'an FECAFOOT. Eto’o mai shekaru 40 ya lashe zaɓen da ƙuri’u…
Read More
Da alamu matar Cristiano Ronaldo ta harbu

Da alamu matar Cristiano Ronaldo ta harbu

Fostin ɗin da ɗan wasa Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na Instagram na cewa matarsa ta samu 'juna biyu. Wannan shi ne fostin na farko da wani ɗan wasa a duniya ya samu mabiya (Likes) mutum miliyan 27 da dubu ɗari ɗaya, kuma yana ci gaba da ƙaruwa ahalin yanzu ashafin Instagram. Ba a iya ƙwallon ƙafa ba, a kowane irin wasa a duniya babu wani ɗan wasa da ya taɓa samun yawan mabiya da suka kai na waɗanda suka bibiyi fostin ɗin na Cristiano Ronaldo wanda ya wallafa a jiya tare da shi da matarsa Georgina.
Read More
A karon farko za a fara gasar daddalla mari a Nijeriya

A karon farko za a fara gasar daddalla mari a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masu shirya wata sabuwar gasa da za a fara a karon farko a Nijeriya, sun ce a fito a fafata domin za a fara gasar mare-mare cikin watan Oktoba a Nijeriya. Babban Daraktan kamfanin tsara wasannin na TKK Sports, Abdulrahman Orosanya ne ya bayyana haka, ranar Juma’a a Legas. Ya ƙara da cewa, ba a dai sa ranar da za a fara ba, amma dai cikin watan Oktoba za a fara, kuma a cikin Disamba za a yi wasannin ƙarshe na cin kofuka. Orosanya ya ce, an ƙirƙiro wannan wasan daddalla mari a ƙasar Rasha, amma…
Read More
Gwamna Sule ya zira ƙwallo a raga a wasan bikin cikar Nasarawa shekara 25 da kafuwa

Gwamna Sule ya zira ƙwallo a raga a wasan bikin cikar Nasarawa shekara 25 da kafuwa

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani ɓangare na cikar Jihar Nasarawa shekara 25 da kafuwa, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abdullahi Sule, ta shirya wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunta inda aka fafata tsakanin ɓangaren Gwamna Sule da ya ƙunshi tsoffin masu buga wa jihar wasa, da kuma ɓangaren tsoffin 'yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙsa, wato Super Eagles. Sanarwar da ta fito ta hannun jami'in yaɗa labarai na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa United, Eche Amos, ta nuna an buga wannan wasa ne a ranar Alhamis da ta gabata a babban filin wasannin motsa jiki da ke Lafia…
Read More
Gerd Muller ya kwanta dama

Gerd Muller ya kwanta dama

Tsohon zakaran ƙwallon ƙafar ƙasar Jus, Gerd Muller, ya rasu. Muller ya bar duniya yana da sheka 75. Bayanai sun nuna a halin rayuwarsa, Muller ya kasance ɗan wasan da ya fi kowa zira ƙwallaye a Bayern Munich inda ya ci ƙwallaye guda 563 a wasanni 605 na Bundesliga, Tun a 2015 aka gano marigayin na ɗauke da cutar Alzheimer, lokacin da yake kocin ƙungiya ta biyu ta Bayern. A wani sako da ta wallafa a shafinta ma Tiwita, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta ce, "Yau duniyar FC Bayern ta tsaya cak. Gwarzon ɗan wasan Jamus da dukkan…
Read More
PSG ta yi babban kamu

PSG ta yi babban kamu

A halin da ake ciki, ya tabbata cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa, Lionel Messi, ya zama ɗan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG. Ƙungiyar PSG ta sanar cewar Lionel Messi ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu bayan barin sa ƙungiyar Barcelona inda ya shafe shekara 21 yana buga mata wasa. Sanarwar PSG ta nuna kwangilar ta kuma ƙunshi buƙatar ƙarin shekara guda bayan kammala shekaru biyun da aka cim ma yarjejeniya idan hali ya yi. Haka nan, cewa Messi zai sanya riga mai ɗauke da lamba 30, lambar da ya yi amfani da ita lokacin da ya fara yi…
Read More
Messi ya yi hawaye saboda alhinin ficewa daga Barcelona

Messi ya yi hawaye saboda alhinin ficewa daga Barcelona

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan, Lionel Messi, ya yi hawayi a baina jama'a saboda alhinin barin ƙungiyar ƙwallon ƙafar da ya shafe shekaru yana buga mata wasa, wato Barcelona. Messi ya zubar da hawaye ne a lokacin da yake ƙoƙarin yi wa taron manema labarai bayani dangane da ficewarsa daga kulob ɗin Barcelona a Camp Nou. A ranar Alhamis da ta gabata Barcelona ta tabbatar wa duniya cewa zakaran ƙwallon ƙafar, ɗan shekara 34 da haihuwa, ba zai sabunta kwantiraginsa da ƙungiyar ba saboda matsalar kuɗi da kuma shirin sake wa ƙungiyar fasali. Messi ya shaida wa manema labarai…
Read More
An shirya wasan sada zumunta na Badminton a Damaturu

An shirya wasan sada zumunta na Badminton a Damaturu

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Sakamakon ci gaba da samun zaman lafiya a Arewa-maso-gabas tare da ma jihar Yobe baki ɗaya, 'yan ƙungiyar wasan Badminton Damaturu sun shirya wasan sada zumunta a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. Da yake jawabi wajen buɗe wasan a ranar Asabar, shugaban kwamitin shirya wasan, Alhaji Bashir Baba Geidam, ya bayyana cewa sun shirya wasan ne domin sada zumunta a birnin Damaturu. Haka kuma, ya ce wannan wasa an saba gudanar da shi ta haɗin gwiwa tsakanin manyan ɓangarorin badminton da ke jihar Yobe, waɗanda suka ƙunshi na Gashuwa, Postiskum da Damaturu a jihar. Bugu…
Read More