Chadi ta saki ’yan tawaye da ’yan adawa 22

Gwamnatin Chadi ta saki wasu ‘yan tawaye da jiga-jigen ‘yan adawa 22 da ake tsare da su bisa zargin cin amanar ƙasa, wanda ke zama kason farko cikin fursunonin da shugaban ƙasar ya yi wa afuwa domin sulhunta ‘yan ƙasar.

Mutanen 22 na daga cikin ‘yan tawaye da jiga-jigen ‘yan siyasa kimanin 296 da shugaban mulkin sojin ƙasar Mahamat Kaka Idris Deby ya sanar da yi mu su afuwa a ƙarshen watan Nuwamba.

Afuwar wanda wani sharaɗi ne da ‘yan adawa suka gindaya domin shiga tattaunawa kan makomar ƙasar mai fama da rikici.

Shugaba Mahamat, mai shekaru 37, wanda ya karɓi ragamar mulkin Chadi bayan da aka kashe mahaifinsa Idris Deby cikin watan Afrilun bara a fagen daga, ya buƙaci tattaunawa da ‘yan tawaye masu ɗauke da makamai.

Wannan ne ya sa ‘yan tawayen suka gindaya sharuɗɗan da a cikinsu suka buƙaci sakin ɗaukacin fursunonin da aka kama a yaƙi, da kuma yin afuwa ga ‘yan adawa tare da maida wa ‘yan tawaye dukiyoyin su da gwamnati ta ƙwace.